Ziyarar Bishop-Bishop na Afurka da Asiya da latin Amurka a Turai | Siyasa | DW | 25.05.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Bishop-Bishop na Afurka da Asiya da latin Amurka a Turai

Bishop-Bishop na mujami'ar Katolika daga kasashen Afurka da Asiya da Latin Amurka na ziyarar kasashen Turai domin ba da kwarin guiwar daukar karin matakai a yaki da matsaloli na talauci da yunwa a duniya

Limaman na mujami’ar katolika daga kasashen Afurka da Asiya da kuma Latin Amurka, wadanda suka kuma sadu da shugaban gwamnati Gerhard Schröder suna da cikakkiyar masaniya a game da mawuyacin halin da Jamus ke fama da shi a game da baitul-malinta, amma duk da haka sun nemi wani kwakkwaran alkawarin cewar kasar zata yi kari akan abin da take kashewa a matakan yaki da matsalar yunwa a duniya. An saurara daga bakin Bishop Oscar Kardinal Rodriguez daga kasar Hondoras yana mai gargadin cewar a yankin Latin Amurka talauci shi ne babbar barazana ga makomar demokradiyya da kwanciyar hankalin jama’a, amma ba juye-juyen mulki na soja ba. Ya kuma kara da cewar:

Wajibi ne a cimma manufofin da aka sa gaba dangane da karnin nan na 21 da muke ciki domin ta haka ne kawai duniya zata samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Muddin aka gaza to kuwa za a sha fama da guje-gujen hijira daga masu fafutukar kyautata makomar rayuwarsu da kuma bunkasar cinikin miyagun kwayoyi. Domin wannan shi ne kafa daya kwal dake taimaka wa kasashe masu tasowa wajen samun kudaden shiga.

A shekara ta 2000 dai, a lokacin taron MDD, dukkan kasashen dake da wakilci a cikinta sun yi alkawarin kayyade matsalar talauci da misalin kashi 50% nan da shekara ta 2015. Kafin wannan lokaci, Jamus na fatan bunkasa yawan taimakon da take bayarwa zuwa kashi 0’7% na jumullar abin da kasar ke samarwa a shekara. Jamus tayi wannan alkawarin ne a cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da kasashen Kungiyar Tarayyar Turai suka bayar baya-bayan nan. A dai halin da muke ciki yanzun duka-duka yawan abin da Jamus ke bayarwa na taimakon raya kasashe masu tasowa bai zarce kashi 0’28% na jumullar abin da take samarwa a shekara ba. Josef Sayer, darektan kungiyar taimakon mujami’ar katolika ta Miseroer ya ce yana fatan ganin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya taka wata rawa ta a zo a gani a game da yaki da matsalar talauci a lokacin taron kolin kasashen G8 da suka fi ci gaban masana’antu a duniya. Kazaliika ya ce yana fatan ganin Schröder yayi amfani da tasirin da yake da shi a kungiyar ciniki ta kasa da kasa WTO domin tabbatar da cewar ana ba da cikakken la’akari ga bukatun kasashe masu tasowa. Babban abin da zai taimaka a shawo kann matsalar talauci da kuma yunwar dake kashe yara kimanin dubu 24 a kowace rana shi ne bunkasa yawan kudaden taimakon raya kasa da yafe wa kasashe matalauta basusukan dake kansu da kuma kamanta adalci a harkokin ciniki na kasa da kasa, kamar yadda bishop-bishop din daga kasashen Afurka da Asiya da kuma latin Amurka suka nunar a lokacin taron manema na hadin guiwar da suka gudanar tare da wakilan kungiyar taimakon mujami’ar katolika ta Miseroer a birnin Berlin. Shugabar CDU Angela Merkel ta tabbatar musu da cewar ba zata mayar da ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa karkashin tutar ma’aikatar harkokin waje idan ta lashe zabe na gaba da wa’adi da ake shirin gudanarwa nan gaba a wannan shekara ba.