Zaben yan majalisar Dottijai a Japan | Labarai | DW | 29.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben yan majalisar Dottijai a Japan

A yau ne ake gudanar da zaben yan majalisar dottijai aaa kasar Japan.Sakamakon jin raayoyin jama da aka gudanar a baya bayan nan dai,ya nunar dacewa jammiyyar Prime minista Shinzo Abe mai mulki a wannan kasa zata sha kaye.Manazarta sun nuni dacewa,idan har Jamiiyyar masu sassucin raayi dake mulki da gaza samun rinjaye a zaben majalisar Dottijan,to dole ne Premier Abe yayi murabus daga mukaminsa,duk dacewa har yanzu jammiiyyarce dake da rinjaye a majalisar wakilai.Gwamnatin Premier Shinzo Abe dai ta fuskanci mummunar suka,sakamakon matsaloli datake fuskanta a yanzu,wadanda suka hadarda da almubazzaranci cikin tsarin biyan Pansio na kasar ta Japan.A watanni 10 da suka gabata nedai Premier Abe ya haye karagar mulki,bayan saukan Junichiro Koizumi daga wannan mukami.