A yayin da ake shirin gudanar da zabe a zagaye na biyu, a jihar Maradi, dan takara Mahamane Ousmane ya sami karin magoya baya.
Magoyan jam’iyyar MNSD Nasara reshen jihar Maradi sun fidda sanarwar ta goyan bayansu ga dan takara Mahamane Ousmane a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da ke tafe.
Abun jira a gani dai, shi ne tasirin ko akasin haka da wannan goyan bayan zai yi a ranar 21 Febrairu mai zuwa, da ake gudanar da babban zaben zagaye na biyu.