Za a sabunta dokokin corona a Jamus | Labarai | DW | 03.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a sabunta dokokin corona a Jamus

Alamu na nuna yiwuwar sake fasalin dokokin yaki da annobar corona a Jamus, sakamakon nazari a kan nasarori da ake gani a kasar bayan tsaurara matakan da mahuknta suka yi.

Gwamnatin Jamus ta ce tana da yakinin cewa mutanen da aka yi wa allurar rigakafin corona da ma wadanda suka warke bayan kamuwa da cutar, za su fita daga cikin rukunin wadanda tsauraran dokokin corona na Jamus zai yi aiki a kan su.

Ministan lafiya a nan Jamus, Jens Spahn, bayan ganawa da shugabar gwamnati Angela Merkel da sauran jiga-jigai, ya ce gwamnati na nazari a kan dabarar bullo da sabbin dokoki a kan yaki da cutar, wadanda za su yi la'akari da batun damar bude shaguna da wasu harkoki.

A cewar minista Jens Spahn, ta yiwu a cimma matsaya a kan hakan a wannan makon inda akalla mutum miliyan uku da suka warke da ma wadanda aka yi wa rigakafin za su fice daga wasu cikin tsauraran matakan.

Wadannan kalamai dai na zuwa ne lokacin da alamu ke nuna raguwa a bangaren wadanda ke kamuwa da cutar ta coronar a nan Jamus.

Sai dai har yanzu kashi takwas ne kadai daga cikin 100 na al'umar Jamus aka yi wa rigakafin cutar kawo yanzu.