Za a janye ′yan sanda daga gidajen attajirai | Siyasa | DW | 21.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Za a janye 'yan sanda daga gidajen attajirai

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya ɓullo da wata doka ta haramta ajiye 'yan sanda a gidajen da ba na hukuma ba.

Gwamnatin ƙasar ta ba da umarnin janye 'yan sanda daga gadin attajirai da sauran masu ruwa da tsaki.Kasa da 'yan sanda dubu 305 ne dai ke ba da tsaro ga al'umma kusan miliyan ɗari 180 a Tarrayar Najeriya, abin kuma da ya kai ga ko wanne ɗan sanda ɗaya na ba da tsaro ga 'yan ƙasar ta Najeriya 600 addadin kuma da ke zaman ɗaya da rabi na addadin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware da nufin tabbatar da isashen tsaro a tsakanin al'umma.

An rage yawan 'yan sandar da ke yin gadi a gidadajen jami'an gwamnati

Abin kuma da ya ɗauki hankalin mahukuntan ƙasar da suka ba da sanarwar rage ba da kariyar 'yan sandan ga jami'ai na gwamnati da kuma janyeta ga waɗanda ba su ruwa da tsaki da harkokin mulkin ƙasar ta Najeriya.Wata sanarwar fadar gwamnatin ƙasar dai ta ce an rage yawan 'yan sandan da ke gadin gwamnoni na jihohi da kaso kusan 50 cikin ɗari sannan kuma an umarci ragewar ga ɗaukacin jami'an mulki a matakai daban- daban.Sabon matakin dai a fadar kakakin gwamnatin ƙasar Femi Adesina na da ruwa da tsaki da ƙoƙarin rage gibin da ke akwai a harkar tsaron cikin gidan ƙasar da ke fuskantar tasku sakamakon giɓin da ya kai na kusan 'yan sanda 20,000 a tsakanin al'umma.

Umarnin ɗaukar ƙarin wasu 'yan sandar daga gwamnatin

Tuni dai dama fadar ta Abuja ta umarci ƙara ɗaukar wasu sabbabin 'yan sandan guda dubu 10,000, duk dai da nufin daɗa inganta rawar 'yan sanda da ake sa ran za su maye gurbin sojoji a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da tsaron cikin gidan a cewar Femi Adesina.“Ka san akwai ka'ida ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ta ce ko wane ɗan sanda zai kare mutane 400. amma a Najeriya ɗan sanda ɗaya na gadin kusan mutum 600.''To sai dai kuma akwai tsoron yiwuwar kwasar bara gurbin da ke iya ƙarewa da zama dillallan laifi maimakon masu ba da kariya ga al'aumma ta ƙasa.

Ya zuwa yanzu dai mahukuntan na Abuja na tsakanin kare attajiran ƙasar ta Najeriya da ke da hannu a cikin shuni, da kuma talakawa da ke ji a jiki sakamakon ƙarancin 'yan sanda dama rashin kwarewar aikinsu.To sai dai kuma a fadar Alhaji Isyaku Ibrahim ɗaya ga jiya yake kallon yau a cikin harkokin ƙasar ta Najeriya, attajiran ƙasar ta Najeriya ba su buƙatar kariya ta musamman in har suna harkokinsu babu son rai a ciki.

Sauti da bidiyo akan labarin