Yunkurin takaita bada mafaka a Jamus | Labarai | DW | 29.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin takaita bada mafaka a Jamus

Hadin kan jam'iyyu da ke mulki a kasar ne suka cimma wata yarjejeniyar yin kwaskwarima ga tsarin neman mafakar siyasa a kasar wanda yanzu ke kan gaba a fiye da ko wace a Turai wajen karban baki

A bara kadai kasar Jamus ta shigar da sunayen mutane miliyan daya da suka nemi a basu mafakar siyasa. Kuma yanzu gwamnati na fatan takaita wannan lamarin. Jagoran jam'iyar SPD Sigmar Gabriel, yace kasashen Moroko, Tunisiya da Aljeriya a sasu a matsayin kasashen da ake zaman lafiya, wadanda ma'ana 'yan kasar basa bukatar mafakar siyasa. Kuma yace a yarjejeniyar da suka cimma za'a dakatar da bada visar hadewar iyalai na shekaru biyu. Kudurin dai na bukatar sa hannun majalisar dokoki da ta zartaswa kan ya zama doka.