′Yan tawayen jam′iyar PDP zasu daukaka kara | Siyasa | DW | 25.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan tawayen jam'iyar PDP zasu daukaka kara

Duk da sabanin ra'ayi tsakanin 'ya'yan sabuwar jam'iyar PDP, akwai alamun zasu daukaa kara a kotu domin kalubalantar kudirin hana yi masu rajista a matsayin jam'iya.

An dai kai ga daukaka kara ana kuma shirin yankan kauna ga 'ya'yan sabuwar jamiyyar PDP da suka ce har yanzu suna da ja, amma kuma suka fara fitar burtu ya zuwa ga jamiyyun adawar kasar ta Najeriya. Duk da cewar dai sun kai har ga gaban manyan mahukuntan shari'ar Tarrayar Najeriya da nufin daukaka kara ta neman bi musu kadi a cikin shari'ar da suka ce bata da adalci, daga dukkan alamu tuni 'ya'yan sabuwar PDP suka fara nuna alamun kai kuna a ci gaban kasancewar su cikin PDP mai mulkin kasar ta Najeriya.

Babu dai zato ba kuma tsammani aka wayi gari da nuna alamun sauyin sheka a bangaren gwamnan jihar Adamawa, dake daya cikin 'yan bakwai na sabuwar PDP da kuma ya tura babban dansa domin share fage cikin APC ta adawa.

Ko bayan Commander Abdul Azeez Nyako mai ritaya da tuni ya bayyana sauyin sheka ya zuwa APC, akalla yan majalisar dokokin jihar 19 da sauran na hannun daman gwamnan Adamawan ne dai suka bayyana aniyarsu ta bin sahu a cikin APC da tayi lale marhabin da sabbabin mabiyan. To sai dai kuma sabbabin matakan da suka biyo bayan kai kawo da taruka a hedikwatacocin jihohin na yan bakwai dai, daga dukkan alamu sun fara daga hankali cikin Gidan Wadata da kewa yunkurin kallon wanda ya saba kaida da dokoki na siyasar kasar a tunanin Barrister Abdullahi Jalo dake zaman mataimakin kakakin PDP da kuma yace har yanzu hanya na bude ga yan bakwai na sulhu tsakani da abokan takun su na baya.

To sai dai shiga APC ko kuma PDM dai daga dukkan alamu han ya zuwa yanzu akwai rabuwar kai a tsakanin bangarorin na sabuwar PDP a tsakanin masu tunanin lokaci yayi na raba gari da masu gidan na wadata da kuma masu ganin har yanzu ana iya turawa a cikin rikicin da ya nufi kotun daukaka karar kasar. Abun kuma da a cewar Bello Sabo Abdulkadir dake zaman jigon na sabuwar PDP ya basu karfin daga kara da nufin tabbatar da adalci da zama na lafiya cikin PDP.

Vize Präsident Atiku Abubakar, Nigeria

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar

To sai dai koma ya zuwa yaushe ne dai fatan na bangaren na sabuwar PDP ke iya tabbata, masana harkokin na siyasa dai na kallon matakan fara sauyin shekar tare da daukar kara zuwa sama a matsayin wani kokari na rabon kafa da nufin kaucewa karewa gida na dana sani. Irin gidan da yai zafi ya kuma kusan kona tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar da yai fada ya ce ya dawo domin sulhu da mai gidan sa chief Olusegun Obasanjo. Matakin kuma da a cewar Garba Umar kari ke iya tsorata masu gidan na wadata na sake zama na zahiri da nufin kaiwa ga biyan bukatunsu

Fade in kari abun jira agani dai na zaman mafita a tsakanin bangarorin dake rikicin da kuma ake saran zasu sake komawa bisa teburi na shawara kowane lokaci daga mako mai kamawa.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin