1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Me ya janyo kaurace wa zabuka?

Nasir Salisu Zango
February 23, 2026

A Najeriya abin da ya faru a zabukan cike gurbi da aka yi a jihohin Kano da Rivers da kuma wanda aka yi na kananan hukumomi a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja, ya bar baya da kura.

https://p.dw.com/p/59I0J
Zabe a Najeriya
Zabe a NajeriyaHoto: Christopher Onah/Focal Point Agency/IMAGO

Mutane basu fito zaben ba a dukkan wadannan wurare lamarin da ya bude shafin fashin baki da masana ke cewar talakawa sun fara dawowa daga rakiyar yan siyasa da ke yawan wadaka da dukiyoyinsu ba tare da tsinana musu wani abin azo a gani ba, sai dai wasu na alakanta rashin fitowar da yanayin jamiyya daya dake neman samun gurni a kasar.

Abubuwan da suka faru

A babban birnin tarayya Abuja rahotanni sun nuna cewar malaman zabe ne suke ta kiran masu zabe kan su zo su kada kuri'un su, a jihar Kano kuwa galiban rumfunan zaben babu kowa sai yan kalilan domin ga jami'an tsaro da ake ganin suna yin karanci a lokutan zabe wannan karon sun ninka masu zabe yawa a wasu wuraren zaben, can ma jihar Rivers haka zancen yake domin galiban mutane sun cigaba da harkokinsu kai kace babu wani zabe da ke gudana.

Zabe a Najeriya
Zabe a NajeriyaHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Lamarin da masu fashin baki irin su Comrade Bello Basi Fagge ke cewar tura ce ta kai bango, kuma idan har ba an yi da gaske ba wannan zabe shi ne makwafin abin da zai faru a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Tuninin sauran masana

Shi ma dai Comrade Auwal Musa Rabsanjani shugaban kungiyar Amnesty international a Nigeria ya ce wannan tutsu da talakawa suka yi yar manuniya ce dake nuna cewar sun fara gazawar su, ga irin mulkin da ake kumahakan shi ne makwafin abin da zai faru a zaben 2027.

Dr Ahmed Saidu Dukawa, masanin kimiyyar siyasa ne a jami'ar Bayero da ke Kano, yace akwai kulalliya wajen gwajin sanya zabe a lokacin azumi amma kuma kacokan wannan rashin fitowar yar manuniya ce dake alamta cewar talakawa sun fara nuna cewar tura ta kai bango.

Tuni dai wannan batu ya zama wani babban lamari da ke jawo cece-kuce da musayar yawu a tsakanin alumma.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani