1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Najeriya dake Nijar sun yi tsokaci kan taron kasa

March 20, 2014

Su ma 'yan asalin Najeriya dake samun mafaka a Nijar ba a bar su a baya ba wajen fadin albarkacin bakinsu dangane da taron kasa a mahaifarsu

https://p.dw.com/p/1BTDF
Flüchtlingsfamilie aus Nigeria bei Diffa Niger
Hoto: DW/Larwana Malam Hami

A yayin da shugaban kasar Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da taron kasa na tsawon watanni uku a matakin farko na warware matsalolin da suka dabai-baye kasar, 'yan asalin tarayyar ta Najeriya dake zaman hijira a yankin Diffa na jamhuriyar Nijar sakamakon tabarbarewar tsaron da ke aukawa a yankunan arewa maso gabashin kasar ne ke bayana ra'ayoyin su game da makomar taron, inda da dama daga cikin su ke cewar taron ba zai tsinana komai ba.

Wadannan 'yan gudun hijira na tarayyar Najeriya da rikicin Boko Haram ya koro kasar ta jamhuriyar Nijar wanda suka samu mafaka a jihar Diffa na ci gaba da maida martani game da makomar taron tamkar takwarorin su na cikin kasar ta tarayyar Najeriya.

A yayin da nake zantawa da su dai 'yan gudun hijirar dake zaune a Diffa sun nuna cewar idan da ana bukatar magance matsalolin da kasar tasu ta asali ke ciki, ba sai an kirayi taron kasa ba kuma shawarwarin da taron zai tsayar ba ra'ayi ba ne na talakawa kamar yadda su Fadimatu Haruna wasu daga cikin yan gudun hijirar ke cewa.

Nigeria Flüchtlinge aus Borno
Hoto: DW

Akwai kyakyawar fata duk da matsalolin da talakawa ke ciki

Duk dai da irin halin kunci da tunani na matsalar tabarbarewar tsaron arewacin kasar ta saka dubban 'yan gudun hijirar gami da raba su da kasar su ta asali tare da ketare iyalai har abadan abada, da dama daga cikin 'yan gudun hijirar dai na bi sau da kafa irin yadda kasar ta kwana da kuma yadda al'amurra ke gudana ta hanyar tuntubar sauran, ta wayoyin salula na jeka da gidanka.

Haka nan kuma duk da cewar wani lokaci ana samun matsalar sadarwa yan gudun hijirar na ci gaba da aike kyawawan fata sadewa da dawamanmen zaman lafiya da zai kasance sakamakon karshen taron kasar dake ci gaba da wakana a yanzu haka.

A yanzu haka dai ba 'yan gudun hijira kadai ba har ma da 'yan asalin kasar dake a Jamhuriyar Nijarr tare kuma da 'yan Nijar na ci gaba da tura adu'o'in cimma matsaya guda a karshen taron domin talakawa su amfana da abun da aka cimma a karshe.

Mawallafi: Larwana Malam Hami
Edita: Pinado Abdu Waba