′Yan gudun hijira sun zama kalubalen siyasar Turai | Labarai | DW | 28.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijira sun zama kalubalen siyasar Turai

A kwai fargabar kara samun sabbin 'yan gudun hijira daga birnin Aleppo da ma wasu yankunan na kasar Siriya bayan lugudan wutar da Rasha a cewar Tusk na kungiyar ta EU.

Bayan da kasashen Turai suke ganin mafi girman kwarara ta 'yan gudun hijira tun bayan yakin duniya na biyu, manyan jami'ai a kungiyar EU sun yi gargadin cewa wannan kwarar baki na iya haifar da babban sauyi a nahiyar adaidai lokacin da kimanin sabbin baki fiye da 700,000 suka isa bakin nahiyar bayan tsallaka tekun bahar rum a cikin wannan shekara.

A cewar Donald Tusk shugaban kungiyar ta kasashen na Turai da yake jawabi ga mambobin kungiyar a Strasbourg akwai fargabar kara samun sabbin 'yan gudun hijira daga birnin Aleppo da ma wasu yankunan na kasar Siriya bayan lugudan wutar da Rasha ke jagoranta a kasar, kalubalen da ya ce zai iya haifar da sauyi a tsarin siyasar ta kasashen Turai kuma hakan ba zai zama abu mai kyau ba ga nahiyar.

Shi ma dai shugaban hukumar kungiyar ta EU Jean-Claude Juncker ya kalubalanci mambobin kasashen kan yadda suke sako-sako wajen cika alkawuran da suka yi a aikin bada kariya ga iyakokinsu tun daga Girka da Italiya.