Yan gudun hijira na yancin mafaka a turai | Labarai | DW | 09.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan gudun hijira na yancin mafaka a turai

Un

Hukumar kula da yan gudun hijira ta mdd ta sanar da tura jamian gani da ido zuwa sansanin baki yan gudun hijira dake tsibirin Lampedusa a kasar Italiya ,wanda ke kann iyaka da arewacin afrika.

A bara dai hukumomin Iltaliyan sunki amincewa jamian hukumar isa yankin,amma a yanzu hukumar kula da yan gudun hijiran tace tana dauke ne da shirin fadakarwa yan gudun hijiran yancinsu na neman mafaka na siyasa.

A bara dai bakin haure akalla dubu 15 suka isa wannan tsibirin akasarinsu kuma yan Afrika,bayan tsira da rayukansu daga matsaloli na jiragen ruwa zuwa masu fataucin mutane.Kungiyoyin kare hakkin jammaa dai sun sha korafi dangane da yadda sansanin na tsbirin Lampedusa ke cika da bakin haure,dake neman shiga turai.