′Yan adawa na sauya sheka a Nijar | BATUTUWA | DW | 24.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

'Yan adawa na sauya sheka a Nijar

A Jamhuriyar Nijar bangarori daban-daban na tofa albarkacin bakinsu dangane da sauya shekar da ake fuskanta a jerin jiga-jigan 'yan adawar kasar tare da mara baya ga bangaren da ke mulki.

UN-Klimakonferenz 2017 in Bonn | Mahamadou Issoufou, Präsident Niger

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Na baya-bayan nan dai shi ne sauya shekar da wasu kusoshin jam’iyyun adawa ciki har da na hannun daman madugun 'yan adawa da na kawancen tsohon ministan harkokin wajen kasar Ibrahim Yacouba. Duk da yake kawo yanzu babu wasu cikakkun alkalumman da ke iya tantance adadin mambobin jam'iyyun adawa da suka hadar da MPN Kishin Kasa ta Ibrahim Yacouba da MDR Tarna da ma Jam'iyyar MODEN-FA Lumana Africa ta madugun 'yan adawar kasar Malam Hama Amadou da suka kai ga sauya shekar zuwa bangaren na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki, bayanai na nuni da cewar cikin wadanda suka bugawa jam'iyyun nasu kyaure da akwai jiga-jigan 'yan adawa irin su Dr Adal Rhoubeid shugaban Jam'iyyar MDR Tarna da kuma kakakin kawancen 'yan adawa na FPR, wanda kuma tuni ma aka nada shi a matsayin mai bai wa shugaban kasa Mahamadou Issoufou shawara na musamman a fadar shugaban kasa.

Duk da yake bai aminta da ya tattauna da manema labarai ba, sai dai a zahiri Dr Adal Rhoubeid ya tabbatar da nadin da aka yi masa kuma shaidawa wakilin DW ta wayar tarho cewa yana cikin juyayi na rasuwa saboda hakan ba zai ce komai kan batun ba. Tuni dai kakakin kawancen na FPR da Dr Adal din ya yi wa adabo, Abdoul Moumouni Ousman ya bayyana ficewar tasa da cewar ba wani tasiri da za ta yi.

Ko bayan Malam Rhoubeid da akwai wani kusa a jam'iyyar MODEN-FA Lumana Africa Ali Gaza Gaza da ke a matsayin tsohon sakataren jam'iyyar ta Lumana da kuma ya balle daga jam'iyyar zuwa PNDS Tarayya a karshen makon da ya gabata, wanda shi ma da aka tuntube shi wayar tarho ya tabbatar da daukar wannan matsayi sai dai ya ce ba zai ce komai ba sai ya shigo birnin Yamai domin kuwa a lokacin yana yankin Dosso.

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin