′Yan adawa a Najeriya sun yi ikirarin bude sabon babi a siyasar kasar | Labarai | DW | 19.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa a Najeriya sun yi ikirarin bude sabon babi a siyasar kasar

A ranar Laraba 'yan majalisa 37 da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyyar PDP, sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar adawa ta APC, wanda hakan ya sa PDP rasa rinjaye a majalisar dokoki.

Babbar jam'iyyar adawa a tarayyar Najeriya ta ce ƙasar za ta samu kyakkyawan shugabanci bayan da jam'iyyar PDP da ke mulki wadda kuma ke iko da gwamnati tun a shekarar 1999, ta rasa rinjaye da take da shi a majalisar dokoki. A ranar Laraba 'yan majalisa 37 da aka zaɓa karkashin jam'iyyar ta PDP, suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar adawa ta APC, wanda hakan ya sa PDP din rasa rinjaye a majalisar dokokin tarayya mai kujeru 360. Kakakin APC Lai Mohammed a wannan Alhamis ya faɗa wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa yanzu an hango wani kyakkyawan fata bayan shekaru 14, yana mai nuni da mamaye harkokin mulki da PDP ta yi a Najeriya tun kawo ƙarshen mulkin soji a 1999. Sai dai manazarta sun ce lokaci bai yi ba da za a ga wani canji mai ma'ana a cikin ƙasar, suna masu saka ayar tambaya ko APC ɗin na da ƙarfin zuciyar da za ta kawo gyara da ake buƙata a cikin harkokin mulkin ƙasar wadda cin hanci da rashawa suka yi wa katutu.

Wallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane