Yawon bude ido wani fanni ne na shigar da kudi aljuhun gwamnati, amma kuma ya na ba wa al'umma damar shakatawa.
Nahiyar Afirka na da kayayyakin tarihi da mutane ke zuwa kallo. Su ma kasashen Turai su na sahu na biyar na wuraren da aka fi zuwa yawon bude ido a duniya. Wata kafa ce ta samar da ayyukan yi da samar wa gwamnati kudi.