1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Gabas ta Tsakiya ya dauki hankalin Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB/ATB
October 10, 2023

Malaman addini a Najeriya sun bukaci ganin sasanta yakin da ya barke tsakanin Isra'ila da Falasdinawa bayan hare-haren da tsagerun kungiyar Hamas suka kaddamar kan kudancin Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4XMGZ
Isra'ila, Re'im | Harin 'yan Hamas kan masu bikin shakatawa
Isra'ila bayan harin 'yan HamasHoto: Jack Guez/AFP/Getty Images

A lokacin da ake ci gaba da kafsa yaki tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, malaman addinin Najeriya sun yi kira ga bangarorin biyu da su tsdagaita wuta domin kare rayyukan fararen hula da yakin ya rutsa da su a wannan yanki nag abas ta tsakiya.

Karin Bayani: Duniya ta yi kakkausar suka a kan harin Hamas

Zirin Gaza | Lokacin hare-haren dakarun Isra'ila
Yankin zirin Gaza lokacin hare-haren dakarun Isra'ilaHoto: Mohammed Talatene/dpa/picture alliance

Najeriya dai kaman sauran kasashen duniya ta shiga damuwa a kan wannan yaki da ake kafsawa tun daga ranar lahadi a tsakanin mayakan Isra'ila da na Falasdinawa, lamarin da ya kasance mafi muni da rabon da a gani tun shekaru 50 ke nan da suka gabata. Damuwa a kan irin abubuwan da ke faruwa a tsakanin bangarorin biyu ya sanya shugabanin addinai a Najeriya sanya baki a cikin lamarin. Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ne shugaban kungiyar Izalatul Bidiah Wa Iqamatul Sunnah Jibwis a Najeriya da ke cewa ya dace a samo hanyar samun zaman lafiya tsakanin su.

Kai hare-hare hare ba kakautawa a tsakanin bangarorin biyu na Isra'ila da Falasdinawa musamman a kan frararen hula dai abin damuwa ne, sanin irin yadda ake zubar da jinin bani adama, abin da mutanen da dama musamman shugabanin addini suka bayyana da bukatar duba karamci da Allah ya yi wa rai na bani Adam da ya kamata a kare shi. Pastor Simon Donli ke zama sakataren kungiyar kristocin Najeriya yankin arewa maso tsakiyar kasar wanda ya nuna muhimmancin zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Isra'ila bayan harin 'yan Hamas | Kibbutz Kfar Aza
Wuraren da hare-haren 'yan Hamas ya shafa a kudancin Isra'ilaHoto: Ronen Zvulun/REUTERS

Hali na kaka nikayi da fararen hula suka shiga a dalilin wannan yaki musamman mata da yara kanana ya kasance abin tashin hankali, musamman yadda duka bangarorin biyu ke amfani da manyan miyagun makamai a kan juna, tuni lamarin ya Sanya mutane da dama barin muhallansu a yayin da da kasashen duniya ke ci gaba da kiran a tsagaita wuta. Duk bangarorin na Israila da Falasdinawa dai na da hulda jakadanci da Najeriya, inda dubban ‘yan kasar ke kai ziyara ta ibada da ma kasuwanci. Wannan ya sanya shugabanin kira ga kasashen duniya da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya na kara kaimi domin ganin Isra'ila da Falasdinawan sun hanzarta rungumar tsagaita wuta da sulhu, domin komai zafin lamari dole a teburin sulhu za a sasanta shi.