Yajin aikin matuka jiragen Lufthansa | Labarai | DW | 04.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin matuka jiragen Lufthansa

Manyan filayen tashi da saukan jiragen sama na Jamus irin su Frankfurt da Düsseldorf ne wannan yajin aiki na kwana daya na matuka jiragen saman Lufthansa ya fi shafa.

Jiragen sama da dama ne aka soke tashinsu a nan Jamus sakamakon yajin aiki da matuka jiragen kanfanin Lufthansa ke gudanarwa, wanda kuma ke zama na 11 a tsukin watanni takwas da suka gabata. Jirage masu cin dogon zango da kuma masu dakon kaya ne yajin aiki ya shafa a filayen tashi da saukan jirage na Frankfurt da Münich da kuma Düsseldorf. Amma kuma za a kammala yajin aiki kafin 12 dare na wannan Alhamis.

Matuka jiragen Lufthansa na nuna adawa da matakin da kanfanin ya dauka na yi wa tsarin yin ritaya gyaran fuska. Makudan kudade ne dai ake asararsu sakamakon yajin aikin, inda jaridar Bild ta ce za ta kai miliyan 25 na Euro a kowace rana ta Allah

Kanfanin Lufthansa ya kaddamar da tsarinsa na jigilar jiragen sama masu saukin kudi bayan da ya hada guywa da wasu kanfanoni irinsu kanfanin jiragen saman Turkiya.

.