Yajin aikin kungiyar malaman jamioi a Najeriya | Labarai | DW | 24.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin kungiyar malaman jamioi a Najeriya

A yau ne malaman jamioi a Najeriya suka shiga yajin aiki na kwanaki 3,a matsayin gargadi,ga gwamnatin taraiya data karya dokar kotu da kuma kin kaddamar da yarjejeniyar biyan albashi da tayi.

Cikin wata sanarwa da kungiyar malaman ta ASUU ta bayar tace,gwamnatin ta kaita makura,saboda hak ata yanke shawar shiga wannan yajin aiki zuwa ranar laraba,wadda daga nan zata duba mataki da zata dauka nan gaba domin tabbatar da anyi mata adalci.

Kungiyar ta ASUU tace hanya kadai ta samun zaman lafiya itace,gwamnati ta shiga tattaunawa da ita game da kaddamar da yarjejeniyar ta 2001 tare kuma da maida malamai 49 da tsohuwar gwamnatin mulkin soji ta kora ba tare da wani sharadi ba.