Yajin aikin gargadi ya samu karbuwa a Jamus | Labarai | DW | 10.04.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin gargadi ya samu karbuwa a Jamus

Babban kanfanin jirgin saman Jamus Lufthansa ya soke tashin jirage 800 bayan da ma'aikatan manyan filayen jiragen saman Francfurt, da Munich, da Koln / Bonn da kuma Bremen suka bi sahu wajen gudanar da yajin aiki.

Kungiyoyin Kogado da dama na Jamus na gudanar da yajin aikin gargadi a wannan Talatar da nufin tilasta wa gwamnati yi wa ma'aikata karin albashi, lamarin da ya yi mummunan tasiri a filayen tashi da saukan jiragen sama na manyan biranen kasar. Babban kanfanin jirgin saman Jamus Lufthansa ya soke tashin jirage 800, wato rabin jiragen da ya kamata su yi jigila bayan da ma'aikatan filayen jiragen saman Francfurt, da Munich, da Koln / Bonn da kuma Bremen suka bi sahu wajen gudanar da yajin aikin.

 A wasu fannoni ma yajin aikin ya samu karbuwa ciki har da matuka bus da jami'an wuraren rainon yara na jihoin North Rhein Westaphalia da Baden-Wüttenberg. Su dai kungiyoyin kodagon da suka hada da Verdi da GEW da DBB suna neman gwamnati ta yi wa ma'aikatanta miliyan biyu da dubu 300 kari kashi 6% ko kuma karin akalla karin Euro 200 na albashi.