1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Bundesliga da wasan cin kofin zakarun Afirka

Gazali Abdou Tasawa MNA
February 3, 2020

Gasar Bundesligar kasar Jamus domin jin yadda ta kaya a karshen mako, a Afirka kuma an buga wasannin kusa da na karshe na ci kofin zakarun nahiyar.

https://p.dw.com/p/3XD0Z
Fußball Bundesliga RB Leipzig - Borussia Mönchengladbach
Hoto: Reuters/M. Rietschel

A cikin shirin na wannan mako za mu leka gasar Bundesligar kasar Jamus domin jin yadda ta kaya a karshen mako, a nahiyar Afirka kuma an buga wasannin kusa da na karshe na ci kofin zakarun Afirka. Muna tafe da karin wasu wasanni da suka hada da damben zamani da kuma musamman kwallon tennis a gasar Ostraliyan Open.

Bari mu yaye labulan shirin namu da gasar kwallon tennis ta Ostraliyan Open.

A ranar Lahadi a birnin Melbourne aka yi karawar karshe ta gasar cin kofin kwallon tennis ta Ostraliyan Open inda aka share awoyi hudu ana gumurzu tsakaninin Novack Djokovic dan kasar Sabiya mai shekaru 32  da kuma Dominic Thiem dan kasar Ostriya mai shekaru 26. Wannan karawa dai wacce aka yi kare jini biri jini a cikinta a gaban dubunnan 'yan kallo ta kawo karshe bayan sabi biyar da nasarar Djokovic wanda ya doke abokin karawar tasa da ci 6-4, 4-6, 2-6, 6-3, 6-4. Sai dai a karshen wasan Djokovic ya ce ya ci zomo, amma fa ya ci gudu inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

"Ya ce kadan da na baras da wannan wasa domin Dominic ba kanwar lasa ba ne a wasan Tennis dan akwai shi da karfi dukar kwallo musamman da hannunsa na dama. Ya ba ni wahala sosai da rikita mani salon wasana. A wani lokacin ma ya fini wasa da kyau. Dan haka duk da nasarar da na samu zan iya cewa a yau babu wani babban gibi tsakaninmu a wasan na yau."

Novak Djokovic (hagu) da Dominic Thiem (dama)
Novak Djokovic (hagu) da Dominic Thiem (dama)Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Wannan dai shi ne karo na takwas da Djokovic ke lashe kofin gasar ta Ostarliyan Open. Wannan nasara ta kuma ba shi damar darewa a kan tebirin kwallon tennis na duniya da maki dubu 9720, Rafael Nadal na Spain na a matsyi na biyu a yayin da Roger Federe na Switzerland ke a matsayin na uku.

A bangaren mata kuwa matashiyar nan ce Ba'amarika 'yar shekaru 21 wato Sofia Kenin ta lashe kofin na Ostarliyan Open bayan da ta doke Garbine Muguruza 'yar kasar Spain a sabi uku 4-6, 6-2, 6-2.

Damben zamani na duniya a Kwango

A daren Juma'a washe garin Asabar a birnin Kinshasa na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, Junior Ilunga Makabu taurarin matashin dan damben zamanin nan na Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango ya kafa tarihi kasancewa dan Kwango Kinshasa na farko da ya lashe kambun damben zamani na duniya na ajin masu matsakaicin nauyi, bayan da a bisa hukuncin alkalai a turmi na 12 ya doke abokin karawarsa Michal Cieslak dan kasar Poland. Wannan shi ne karo na 25 da Ilunga Makabu ke nasara a dambe 27 da ya kara.

Wasannin Bundesligar kasar Jamus

Erling Haaland (hagu) ya kafa bajintar kasancewa dan wasan da ya ta ba cin kwallaye bakwai a wasanni uku a tarihin Bundesliga
Erling Haaland (hagu) ya kafa bajintar kasancewa dan wasan da ya ta ba cin kwallaye bakwai a wasanni uku a tarihin BundesligaHoto: picture-alliance/L. Perenyi

A karwar da aka yi a ranar Asabar tsakanin kungiyar Hoffenheim da kuma Leverkusen a wasannin mako na 20 na Bundesliga, inda mai masaukin baki Hoffenheim ta doke Leverkusen da ci biyu da daya. Wani wasan da ya dau hankali shi ne cin kacar tsohon keke da Yaya karama Borussia Dortmund ta yi wa Union Berlin da ci biyar da nema, wasan da a cikinsa sabon matashin dan wasan nan na kasar Norway mai shekaru 19, Erling Haaland, wanda Dortmund ta cefano a karshen shekarar da ta gabata, a farashin ragon malam na kudi miliyan 20 na Euro kacal, ya sake cin kwallaye guda biyu. Lamarin da ya ba shi damar kafa bajintar kasancewa dan wasan da ya ta ba cin kwallaye bakwai a wasanni uku a tarihin Bundesliga. Sai dai duk da haka kungiyar ta Dortmund na a matsayin ta uku a tebirin Bundesliga da maki 39, Leipzig wacce da kyar da jibin goshi ta kwaci kanta a gida inda ta tashi 2-2 da Mönchengladbach na a matsayin ta biyu da maki 41 a yayin da mai abu ya karbi abinsa inda "Yaya Babba" Bayern Munich wacce ta casa Mainz da ci 3-1 ta karbe saman tebirin na Bundesliga da maki 42.

Kofin zakarun Afirka

Har yanzu dai muna kan batun kwallon kafa amma a wannan karo a nahiyar Afirka inda  a gasar cin kofin zakarun Afirka ta shekara ta 2019-2020 da aka buga a karshen mako, an san a yanzu kungiyoyi takwas da suka samu tikitin zuwa wasanni kwata final na gasar. Wadannan kungiyoyi su ne Esperance ta Tunis da Etoile Sportive du Sahel daga Tunusiya, Tout Puissant Mazembe ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, Memelodi Sundowns daga Afirka ta kudu, Zamalek da Al-Ahli daga Masar, sai Raja Casablanca da Wydad Casablanca daga Maroko. A ranar Laraba mai zuwa ce hukumar kwallon kafa ta Afirka wato CAF za ta fitar da jadawalin wasannin na kwata final.