1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Bundesliga da gasar tseren motoci

Suleiman Babayo MNA
January 11, 2021

A cikin shirin akwai sakamakon wasannin karshen mako a lig na Jamus da ake kira Bundesliga da wasu wasanni sannan Kamaru za ta dauki bakoncin wasan matasa na Afirka gami da wasu fannonin.

https://p.dw.com/p/3nn8L
Deutschland Bundesliga RB Leipzig - Borussia Dortmund | Tor Sancho
Hoto: Michael Sohn/AP Photo/picture alliance

Za mu dauko shirin da sakamakon wassin lig na Jamus da ake kira Bundesliga inda Leverkusen  da Bremen suka tashi ci daya da daya. Freiburg ta doke Kwalan da ci 5 da nema. 
Union Berlin 2 Wolfsburg 2. Ita kuwa Mainz an bi ta gida ne aka fi ta iya rawa da ci biyu da nema a hannu  Frankfurt. Ita kuwa Schalke 04 a karshe ta yi nasara, inda ta buge Hoffenheim da ci 4 da banza. A sauran wasannin RB Leipzig 1-Dortmund 3, Augsburg 1-Stuttgart 4, Arminia Bielefeld 1-Hertha Berlin 0, Mönchengladbach 3-Bayern 2. 

Har yanzu Bayern Munich ce ke a saman teburin Bundesliga da maki 33, sai Leipzig mai maki 31, Leverkusen maki 29, Dortmun 28 sai a Union Berlin a matsayi na biyar da maki 25.

Jack Aitken dan wasan tseren motoci na Formula One, mai ruwa biyu na kasashen Birtaniya da Koriya ta Kudu, ya nuna jin dadi da irin sakonnin da ya samu na karfafa gwiwa daga Koriya ta Kudu bayan da ya shiga gasar ta shekarar da ta gabata ta 2020, sakamakon nasarar da ya samu lokacin da Jack Aitken ya maye gurbin George Russell wanda shi ma tun farko ya maye gurbin Lewis Hamilton, wanda aka gwada yana dauke da cutar coronavirus a tawagar motocin kirar Mercedes.

Jack Aitken a lokacin gasar Formula One a Bahrain a watan Disamban 2020
Jack Aitken a lokacin gasar Formula One a Bahrain a watan Disamban 2020Hoto: Giuseppe Cacace/AFP/Getty Images

Jack Aitken wanda mahaifinsa dan Birtaniya kuma mahaifiyarsa 'yar Koriya ta Kudu ya zo matsayi na 16 a gasar da ta wakana a Bahrain.

A kasar Amirka ana sa ran Shugaba Donald Trump mai barin gado zai bayar da lambar girmamawa mafi girma na kasar ga Bill Belichick, kocin kungiyar New England Patriots daya daga cikin kungiyoyin kwallon Amirka masu tasiri.

Kamaru ta ce a shirye tsaf domin karbar bakwancin gasar cin kofin Afirka na matasa masu buga kwallo a gida CHAN gasar da za a fara ranar Asabar.

Mai horas da 'yan wasan Cricket na kasar Pakistan Misbah-ul-Haq ya ce makomarsa na hannun hukumar kula da wasanni ta kasar bayan kasar New Zealand ta samu galaba kan Pakistan a wasan da kasashen biyu suka kara na Cricket. Shi dai Misbah-ul-Haq ya rasa samun nasara a wasanni uku, a duk wasannin kasashen ketare a watanni 15 da yake rike da mukamun abin da ya janyo rade-radin za a iya korarsa daga bakin aiki.