Warware rikicin tsaron kasashen yammacin Afirka | Siyasa | DW | 12.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Warware rikicin tsaron kasashen yammacin Afirka

Ana ci gaba da samun martani kan neman kafa wata rundunar hadin gwiwa a kasashen yammacin Afirka renon Faransa domin magance tsaro.

A Jamhuriyar Nijar bangarori daban-daban da suka hada da 'yan farar hula da masu sharhi kan tsaro na tsokaci kan yunkurin kafa wata rundunar sojojin kasa da kasa da za ta yaki ta'addanci a yammacin Afirka da shugabannin kasashen suka ba da shawara a wani taron kolin da suka yi.

A yayin taron kolin kasashen biyar na renon Faransa ne dai da aka kammala shugaban kasar Nijer Issoufou Mahamadou ya bukaci kasashen da su tashi tsaye da kansu don yin fito na fito da ayyukan ta'addanci da ke addabar kasashen duba da abubuwan da ke faruwa yanzu hakan tsakanin kasashen Mali da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita inda hare-haren ta'addanci ya yi kamari musamman a iyakokin Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso baya ga wani harin na kasar Cote d'Ivoire da ya halaka jama'a masu yawa, Malam Ibrahim Yacouba shi ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar ya ce tuni wannan shawara ta samu karbuwa.

Sai dai tuni wasu masu sharhi ke ta tabka mahawara kan wannan yunkuri musamman ma duba da yanda al'amurra ke tafiya yankin tabkin Chadi inda wata runduna ta kasa da kasa tsakanin kasashe biyar suka gasa cimma gurinsu na kawar da ayyukan kungiyar Boko Haram Malam Moussa Tchangari na kungiyoyin Alternative na mai ganin cewar shuwagabannin kasashen kamata ya yi su yi wa batun karatun tanatsu kana su sauya akida .

Wani dan jarida kuma mai sharhi akan al'amurran tsaro Malam Moussa Aksar na mai ganin cewar matakin da shugabannin kasashen ke shirin dauka zai taimaka ainin ganin 'yan ta'adda na kara kwararo daga kasashen Libiya da Mali domin samun gindin zama a wasu kasashen masu raunin karfi sojoji.

Yanzu hakan dai kasashe kamar su Jamhuriyar Nijar na da kimanin sojoji 900 da ke arewacin Mali yayin da Burkina Faso ke da fiye da 1,500 inda suke aikin kwantar da tarzoma duk da hare-haren da kasashen ke fuskanta na 'yan ta'adda abubuwan da suka janyo shugabannin nuna matukar bukatar kara kyautata matsayin rundunar Munisma a Mali inda 'yan ta'adda suka yi tunga. Hukumomin na zargin hare-haren ta'addancin da duk suka faru a baya-bayan nan a kasashen Burkina da Cote d'Ivoire an kitsa su ne da gamin bakin 'yan ta'adda da suka samu mafaka a Mali.

Sauti da bidiyo akan labarin