Wani jirgin yaki ya kashe mutane 30 a Nijar | Labarai | DW | 18.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani jirgin yaki ya kashe mutane 30 a Nijar

Wani jirgin saman yaki da ba a san asalinsa ba ya jefa bam kan iyakar Nijar da Najeriya inda ya halaka mutane gommai da ke zaman makoki a garin Abadam.

Mutane kimanin 30 da ke zaman makoki aka kashe lokacin da wani jirgin sama da ba a san asalinsa ba ya jefa bam kan wani kauyen Nijar da ke kusa da iyaka da Najeriya. Lamarin ya faru ne a ranar Talata amma sai a wannan Laraba jami'ai a Bosso suka ba da labarin. Wata majiyar kungiyar agaji ta ce mutane 20 zuwa 30 aka kashe a harin da ya auku kusa da wani masallaci a kauyen Abadam kuma dukkan wadanda abin ya shafa mazauna yankin ne da ke zaman makokin wani jami'i. Ba a san wanda ya kai harin ta sama a Nijar ba, amma Najeriya ta ce ba ita ba ce, inji kakakin rundunar mayakan saman Najeriya Air Commodore Dele Alonge. Sai dai wani shugaban yankin da ya ce wadanda suka mutu sun kai mutum 37 sannan 20 sun jikkata, ya dora laifin kan sojojin Najeriya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar