Wani hari a gabashin kasar Jamhuriyar Nijar ya hallaka mutane uku | Labarai | DW | 28.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani hari a gabashin kasar Jamhuriyar Nijar ya hallaka mutane uku

'Yan Boko Haram, sun kai hari a garin Abadam da ke cikin jihar Diffa a gabashin Jamhuriyar Nijar, inda suka hallaka mutane uku cikinsu har da wani sojan Nijar daya.

Wannan harin ya wakana ne tun a farkon wannan mako amma kuma sai a yammacin jiya Alhamis aka samu labarin daga wata majiya ta jami'an tsaron kasar. A kalla dai 'yan gudun hijira dubu 150 ne da suka guje wa yakin da ake da Boko Haram daga Najeriya, ke a yankin Jihar Diffa, inda gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Nijar ta saka dokar ta-baci, tare kuma da kame mutanen da ake zarki da alaka da 'yan kungiyar ta Boko Haram da yawansu ya kai mutune 1.100 kawo yanzu.