1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Von der Leyen ta tabbatar da sake neman takara

Abdullahi Tanko Bala
February 19, 2024

Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce za ta sake neman shugabancin hukumar a wa'adi na biyu

https://p.dw.com/p/4cabs
Deutschland | Münchener Sicherheitskonferenz | Präsidentin der Europäischen Kommission, Ursula von der Leyen
Hoto: Markus Fischer/IMAGO

'Yar siyasa kuma tsohuwar ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta tabbatar da aniyar neman shugabancin hukumar tarayyar Turai a wa'adi na biyu kamar yadda Jam'iyyarta ta CDU ta sanar 

Shugaban jam'iyyar ta CDU Friedrich Merz ya shaida wa taron yan jarida a Berlin cewa Jam'iyyar ta tsayar da von der Leyen domin sake neman mukamin ba tare da wata hamaiya ba.

Ana sa ran sanar da tsayawarta takara a hukumance bayan taron jam'iyyar da ta ke kawance da ita EPP ta gudanar da taron a farkon watan Maris mai kamawa.

Von der Leyen na rike da shugabancin hukumar tarayyar Turai tun shekarar 2019, inda ta jagoranci hukumar cikin kalubale da suka hada da annobar Corona da yakin Rasha da Ukraine.

Ita ce mace ta farko da ta jagoranci kungiyar kolin ta tarayyar Turai.