Venezuela ta sallami jakadan Jamus
March 6, 2019Talla
Gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro, ta debar wa jakadan na Jamus Daniel Kriener sa'o'i 48 da ya bar kasar, saboda saba ka'idojin tsarin diflomasiyyar kasashe.
Sallamar jakadan na Jamus a Venezuela dai na zuwa ne kwanaki biyu da marabtar madugun adawar kasar Juan Guaido da ya yi, a filin jirgi na birnin Caracas.
Tuni kuwa ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta sanar da labarin sallamar babban jami'in na ta na diflomasiyya a Venezuelar, tana mai cewa tana kan tuntubar kawayenta dangane da wannan batu.
Kasar Venezuela dai na cikin rikicin shugabanci, inda wasu manyan kasashen duniya suke goyon kawo karshen mulkin Shugaba Nicolas Maduro tare da amince wa Juan Guido ya rike gwamnatin riko.