Unicef ta nuna damuwa kan kisan kananan yara a Sahel | Labarai | DW | 28.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Unicef ta nuna damuwa kan kisan kananan yara a Sahel

Asusun Unicef ya bayyana damuwa kan kashe-kashen kananan yara a tashe-tashen hankulan da ke faruwa a kasashen tsakiyar yankin Sahel musamman a kasar Mali.

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya wato Unicef ya bayyana damuwa kan yadda aka fuskantar kashe-kashen yara kanana da raba su da iyayensu a tashe-tashen hankullan da ke wakana a kasashen tsakiyar yankin Sahel na Mali, Burkina Faso da Nijar.

A wani rahoto da ya fitar a wannan Talata asusun na Unicef ya ce a kasar Mali kadai an halaka kananan yara 277 ko kuma nakasa su a watanni tara na farkon shekara ta 2019, adadin da ya nunka gida biyu na shekara ta 2018.

Asusun na Unicef ya ce ko da shike cewa a halin yanzu alkalumman kasar Malin ne kawai yake da a hakumance kan wannan mummunan yanayi da yaran ke ciki, a kasashen Burkina Faso da Nijar ma akwai darururuwan kananan yaran da suka tsinci kansu a cikin irin wannan matsala, inda ko baya ga kashe su, mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda ke sace su, suna yi masu fyade ko kuma tilasta masu shiga yaki.