Turkiyya ta bukaci Jamus ta kama Saleh Muslim | Labarai | DW | 05.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya ta bukaci Jamus ta kama Saleh Muslim

Kasar Turkiyya ta bukaci Jamus da ta kama Saleh Muslim jagoran Kurdawa na Siriya, wanda aka tsare a makon jiya a birnin Prague kafin daga bisani a salemeshi.

Bayan an sakeshi,Saleh Muslim ya isa a kasar Jamus,kuma Turkiyya na zarginsa da hanun a wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota, a shekara ta 2016 a birnin Ankara wanda a ciki mutane 36 suka mutu. Ministan harkokin waje na Turkiyya ya ce zai tattauna batun, a gobe Talata, tare da takwaransa na Jamus Sigmar Gabriel.