1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta amince da tsagaita wuta a arewacin Siriya

Mahamud Yaya Azare LMJ
October 17, 2019

Ana ci gaba da matsin lamba ga shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan kan ya dakatar da farmakin da dakarunsa ke kai wa a yankin Kurdawa da ke Arewa maso Gabashin Siriya. Turkiyyar dai ta amince da tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/3RTJJ
Militärischer Konflikt in Nordsyrien | Türkischer Präsident Recep Tayyip Erdogan mit US-Vizepräsident Mike Pence
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Presidential Press Service

Rahotanni sun nunar da cewa Turkiyya ta amince da ta tsagaita wutar ne, bayan da tawagar da mataimakin shugaban Amirkan Mike Pence ke jagoranta, da ta kunshi Sakataren harkokin wajen Amirkan Mike Pompeo da wasu manyan jami'an gwamnatin Amirkan ta isa Ankara har ma ta fara ganawa da wasu daga cikin jami'an gwamnatin kafin daga bisani shugaban tawagar kana mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence ya isa fadar gwamnatin Turkiyyan domin ganawa da Shugaba Recep Tayyip Erdoğan. Tawagar dai ta isa Tukiyyan ne a wani yunkuri na shawo kan mahukuntan Ankaran dasu dakatar da farmakin da dakarunsu ke kai wa a kan Kurdawan da ke Siriya ko kuma ta fuskanci sabon takunkumi, kamar yadda Kakakin fadar shugaban Amirkan  Kelly Craft ya bayyana, inda ya ce tawagar ta je ne domin ta yi rarrashi da kuma kashedi a lokaci guda. Da yake ganawa da 'yan jami'yyarsa ta AKP a birnin Ankara, Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyyan ya ce ba shi da aniyar ganawa da wannan tawagar ta Amirka, yana mai gindaya wasu sharudda da za su sanya dakatar da wannan farmaki nasa a yankin na Kurdawan Siriyan in har an cika su. Sai dai tuni Erdogan din ya karbi bakuncin  Mike Pence a fadarsa, inda za su gana.

Mike Pence und Mike Pompeo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Martin

Duk hakan dai na gudanane a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke nuna damuwarta da rahotannin da ke nuni da cewa, mayakan sa kai na Kurdawa da a baya Amirka ta yi amfani da su wajen yakar kungiyar IS ta yan ta'adda, sun jingine batun yakar IS din, inda suka koma yakin kare kansu daga abun da suka kira mamamya da harin cin zalin Turkiyya. A hannu guda kuma  dakarun Siriya wadanda 'yan sandan kwantar da tarzoma na Rasha ke dafa musu baya, sun kame garin Minbij da Turkiyyan ke son mayar da shi cibiyar tsuganar da 'yan gudun hijira, lamarin da ya janyo ake nuna fargabar samun taho mu gama tsakanin bangarorin da ke ikirarin sun shiga kasar ne don ceton al'ummar Siriya, da a halin yanzu ke ci gaba da dandana kudarta sakamakon wannan sabuwar takaddamar.