Turai ta kara takunkumi kan Rasha | Labarai | DW | 12.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai ta kara takunkumi kan Rasha

Kungiyar Tarayyar Turai ta kara tsaurara matakan takunkumi kan Rasha

A wannan Jumma'a kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana kara tsaurara takunkumi kan kasar Rasha bisa fannin da suka shafi kudade, da makamai da kuma harkokin makamashi, saboda yadda mahukuntan birnin Moscow ke kara sukurkuta lamura a gabashin kasar Ukraine.

A wani zama na jiya Alhamis aka amince da sabbin matakan, inda aka fadada takunkumin daga bankunan Rasha zuwa kamfanonin mai na kasar, da rufe asusun ajiya na wasu manyan jami'ai 24.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba