Turai ta goyi bayan WHO, ta sabawa Trump | Labarai | DW | 19.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai ta goyi bayan WHO, ta sabawa Trump

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta nuna goyon baya ga ayyukan hukumar lafiya ta duniya, WHO, a yakin da take yi na neman murkushe coronavirus.

Matsayar EU ta fito ne a wannan Talata bayan a ranar Litinin Shugaba Donald Trump na Amirka ya rubuta wata wasika, inda ya yi kaca-kaca da WHO, yana mai zargin hukumar da zama 'yar koren kasar China. 

Sai dai mai magana da yawun Sashen Kula da Kasashen Waje na EU, Virginie Battu-Henriksson ya shaida wa 'yan jarida cewa yanzu lokaci ne na nuna 'yan uwantaka ba nuna dan yatsa ga wani a kan cutar corona ba. A don haka EU  ta bayar da karin tallafin kudi ga WHO domin ba hukumar damar sauke nauyin da ke kafadarta, matsayar da ta sabawa Shugaba Donald Trump na Amirka wanda ya kwashe watanni yana sukar ayyukan hukumar ta WHO.