Turai ta amince da takunkumin Rasha a hukumance | Labarai | DW | 31.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai ta amince da takunkumin Rasha a hukumance

Bayan da ta yi ta jan kafa, tarayyar Turai ta amince ta kakabawa Rasha takunkumin da zai shafi sassan Hada-hadar kudi da tsaro da makamashi

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da takunkumin karya tattalin arzikin Rasha a hukumance, da nufin ganin ta dauki alhakin rikicin Ukraine, ta kuma yi nadama ta sauya alkiblarta.

Wadannan sabbin matakai, wadanda aka amince da su daga farkon wannan makon bayan da aka dauki watanni ana jan kafa, ya shafi bankuna ne da sassan tsaro da na makamashi.

A wata sanarwrar da ta fitar, wanda kamfanin dillancin Labaran AFP na Faransa ya gani, ta ce matakin farko shi ne ragewa bankunan samun daman yin ma'amala da kasuwannin hada-hadar kudin Turai, musamman birnin Landan, wanda zai kara musu farashin yin hada-hada ya kuma rage musu karfin gudunmawar da suke baiwa tattalin arzikin kasa

Takunkumin dai ya tanadci haramcin saye da sayar da makamai da fasahohi masu sarkakiya, an kuma hana saidawa bankunan Rashawan, hannayen jari, da takardun lamuni da ma damar cin bashin da zai nuna a tsukin kwanaki 90. Sai dai takunkumin bai shafi iskar gas ba, wanda Rashar ke baiwa Turai kashi biyu cikin uku na iskar gas din da nahiyar ke amfani da shi.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman