Turai: Baki dubu 700 sun samu mafaka | Labarai | DW | 26.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai: Baki dubu 700 sun samu mafaka

Sama da kashi 70 cikin dari na wadanda suka nemi mafakar siyasar dai a Jamus sun sami wannan dama daga mahukuntan kasar ta Jamus abin da ya sanya kasar ta yi zarra tsakanin takwarorinta na Turai.

Kasashe mambobi na Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da bada mafakar siyasa ga baki 710,400 a shekarar 2016, adadin da ke zama ninki ba ninki na abin da aka amince da shi a shekarar 2015. Sama da 'yan gudun hijira dubu 400 ne dai daga Siriya suka samu mafakar siyasa a Jamus.

Sama da kashi 70 cikin dari na wadanda suka nemi mafakar siyasar dai a Jamus sun sami wannan dama daga mahukuntan kasar ta Jamus abin da ya sanya kasar ta yi zarra tsakanin takwarorinta na Turai wajen karbar bakin.

Kasa ta biyu da ke bin ta Jamus wajen karbar 'yan gudun hijirar na zama  Swedenda ta karbi kusan dubu 70 kana Italiya mai sama da mutane dubu 35.

Kasar Poland dai ta bada mafaka ga baki 390 ne abin da ke sa ta zama baya cikin kasashen na EU wajen bada mafakar ta siyasa.