1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin Jamus da Rasha

April 30, 2014

Rikicin Ukraine ya kawo gurbacewar dangantaka tsakanin kasashen Jamus da Rasha, wadanda bisa al'ada suke da kusantar juna tsakaninsu a fannonin siyasa da tattalin arziki

https://p.dw.com/p/1Brd1
Gerhard Schröder und Wladimir Putin
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun bayan da Rasha ta maida yankin Kirimiya na Ukraine karkashin mallakarta, sa'annan yan tawaye masu goyon bayan Rashan suka kama, kuma suke ci gaba da garkuwa da maa'aikatan hukumar tsaro da hadin kan Turai, wato OSCE a gabashin Ukraine, dangantaka take kara tsami tsakanin kasar ta Rasha da Jamus. Shugaban gwamnati, Angela Merkel tana ci gaba da gargadin shugaban Rasha, Vladimir Putin, game da take-takensa kan Ukraine, yayin da kasar ta shiga jerin takwarorinta na kungiyar hadin kan Turai, domin dorawa Rashan takunkumi.

Lokacin wani biki da kamfanin Nord Stream AG ya shirya a garin St. Petersburg na Rasha, shugaban kasar Vladimir Putin ya gana da babban abokinsa daga Jamus, kuma tsohon shugaban gwamnati, Gerhard Schröder, wanda ma saboda shi ne aka shirya bikin a St. Petersburg, a matsayinsa na shugaban kwamitin masu hannayen jari a wannan kamfani, wanda mafi yawan jarinsa yake hannun gagarumin kamfanin nan na gas na Rasha, wato Gazprom.

Hotunan da aka nuna a game da wannan gagarumin biki da abokantaka mai karfi tsakanin shugabannin biyu, ana iya fassara su da cewar akwai dangantaka mai karfi tsakanin kasar ta Rasha da Jamus, saboda ko da shike Gerhard Schröder, ya janye daga al'amuran siyasa, amma jam'iyyarsa ta Social Democrats ta kasance wani bangare na gwamnatin hadin gwiwa ta tarayya dake mulki yanzu. Kazalika, daya daga cikin manyan makusantan Schröder, Frank-Walter Steinmeier, shine alhakin tsara manufofin harkokin wajen Jamus ya rataya a wuyansa. To sai dai a zahiri, rikicin kasar Ukraine, ya kawo canji matuka a dangantaka tsakanin kasar ta Rasha da Jamus. Ganin cewar a da Jamus ta taba zama kasa mafi muhimmanci a matsayin kawar Rasha a tsakanin kasashen yamma, ya sanya Hans Joachim-Spanger, shugaban cibiyar nazarin zaman lafiya da sulhunta rikice-rikice dake jihar Hesse yake cewa:

Putin und Merkel bei der Hannover Messe
Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban gwamnatin Jamus, Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa

"Jamus ta taba zama kasar dake da fifiko a huldodi tsakanin Rasha da kungiyar tsaro NATO da Kungiyar Hadin Kan Turai, abin da hakan ya kawo daga matsayin Jamus a idanun duniya. A daya hannun, ministan harkokin waje, Frank-Walter Steinmeier yana ci gaba da kokarin ganin jawabansa sun kasance masu sassauci a irin wannan hali da aka shiga na rashin fahimtar juna, yadda za'a ci gaba da samun tuntuba da fahimtar juna. Wannan kuwa shine kadai abin da ya rage a fifikon da jamus take dashi."

Shi kuwa Alexander Dykin, darektan sashen nazarin tattalin arzikin da dangantka tsakanin kasashen duniya, a cibiyar nazarin kimiyya da siyasa ta Rasha, ya duba irin rawar da Jamus take takawa a rikicinm gaba daya ne ta wata fuskar dabam.

Yace Jamus da alamu bata yi amfani da matsayinta na kasar dake da fifiko ba, domin ganin an kawo karshen rikicin da ake fama dashi yanzu.

Masanin na Rasha yace kasashen yamma sun kasa gabatar da wasu manufofi na kansu, ba tare da sai sun kyale Amirka ta shimfida masu matakan da zasu rika dauka ba.

Wakilin musamman na gwamnatin taraiya a dangantaka da Rasha, Gernot Erler ya bada shawarar shirya wani sabon zagayen shawarwari tsakanin kasashen yamma da Rasha, saboda kamar yadda yace: akwai abubuwa masu tarin yawa da bangarorin biyu ya kamata su tattauna a kansu. Alexander Dykin yace bisa manufa, yana goyo bayan irin wannan tattaunawa, ko da shike a ganawar farko da aka yi a Geneva, bangarorin biyu sun kasa bullo da wasu matakai da zasu tabatar da ganin an aiwatar da tsarin yarjeniyoyin da suka amince dasu.

Porträt Gernot Erler
Gernot ErlerHoto: picture-alliance/dpa

A fannin tattalin arziki, Alexander Dykin da Joachim Spanger sun daidaita kan cewar Jamus da Rasha suna bukatar hadin kai da juna, inda ma kamfanoni da masana'antun Jamus yanzu haka suke gwagwarmayar ganin kasashen Turai basu kai ga dorawa mataki na uku na tatkunkumin da sukai barazanar dorawa kasar saboda rikicin Ukraine ba.

Mawallafa:Markus Lütticke/Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman