1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tinubu ya zargi siyasantar da aikin kwadago

March 1, 2024

Bayan tsawon lokaci ana danyen ganye, daga dukkan alamu ana shirin raba gari tsakanin Kungiyar Kwadagon Najeriya da ke saurin fushi da gwamnatin kasar da ke nunin yatsa.

https://p.dw.com/p/4d5GR
Bola TinubuHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Tura dai daga dukkan alamu tana shirin kai bango ga shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da ke fadin ana ta siyasa cikin batu na kodago cikin kasar.

Tinubun dai ya zargi masu kwadagon da sauyin launin fafutukar inganta rayuwar ma'aikatan zuwa taka rawar kida irin na adawar cikin kasar a halin yanzu.

Wannan ne dai karo na farkon fari da shugaban yake aiken sako ga masu kodagon da tun da farkon fari gwamnatin kasar  ta dauki lokaci tana lallashi.

Nigeria Abuja | Protest für Mindestlohn vor Nationalversammlung
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Kungiya ta kwadagon kasar NLC dai na da ruwa da tsaki cikin kafuwar Labour Party da ke zaman daya a cikin manyan jam'iyyun da ke cikin batun na adawa mai zafi cikin kasar a halin yanzu.

To sai dai kuma daga dukkan alamu kalaman na shugaban na shirin yin fami bisa tsohon mikin gwagwarmaya ta kodago cikin kasar a halin yanzu.

Dr Muttaka Yusha'u dai na zaman shugaba na gangami da wayer da kai a kungiyar ta NLC, kuma ya ce babu gudu basu shirin jan baya a kokari na neman gyaran lamura cikin kasar.

Koma ya zuwa ina ake shirin a kai  cikin sabon rikicin dai, sai dai da ta kai ga dakatar da kungiyar NLC tare da sa mata kantoma da nufin rage kaifin adawa da rawar sojoji cikin batu na mulki na kasar.

Nigeria | NLC Protest
Hoto: Nasir Salisu Zango

To sai dai kuma an dauki lokaci ana zargin masu kodagon da hawa wuyan fafutukar cikin gari, a kokari na kaiwa ga bukatun son rai cikin  kasar d ata kallo rikidewar masu kodagon zuwa manyan attajirai ciki dama wajen batun na siyasa.

Dr Faruk BB  Faruk dai na  sharhi a cikin harkar mulki, kuma ya ce gugar zana ta shugaban na zaman alamun jefa masu kwadagon cikin aljihu na gwamnatin.

Danyen ganye a kokari na kau da hankalin talakawa, ko kuma kokari na neman daidai a bangare na  masu kodago, sabo na mataki na gwamnatin a tunanin Kabiru Shehu Dakata da ke gwagwarmaya ta kare rayuwar al'umma na zaman alamun dai dai cikin tafiyarwa ta kungiya ta kodagon kasar.

Nan da tsawon makonni guda biyun dake tafe ne dai al'ummar tarrayar najeriyar ke kallon tasirin sabuwar barazana ga masu kodagon dake shirin komawa ga tituna cikin matsa lamba ga masu mulki na kasar.