1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawunan 'yan kodagon Najeriya sun rabu

February 22, 2024

Mako guda da fara zanga-zangar cikin gari daga 'yan kodagon Tarayyar Najeriya, ana hango rabuwa a tsakanin manyan kungiyoyi na kodagon kasar guda biyu.

https://p.dw.com/p/4clwp
Najeriya | NLC | Abuja | TUC | Zanga-Zanga
Zanga-zangar 'yan kodago a AbujaHoto: Uwais/DW

Wata wasika a bangaren TUC ta manyan ma'aikatan kasar dai, ta zargi 'yar uwar tata NLC da yin gaban kanta. A sati na biyu na watan Fabarairun nan ne dai NLC ta bai wa Abujar wa'adin makonni biyu, ko dai ta cika alkawari tare da tabbatar da makaman rage radadin rayuwa ko kuma masu kodagon su fada titi a tsakanin 27 zuwa 28 na watan da nufin nuna bacin ransu. NLC dai ta sa kafa ta shure duk kokarn jami'an tsaron kasar na sanyaya gwiwa a wajen zanga-zangar da ke zaman irinta ta farko, tun bayan rikicin tattalin arzikin kasar da ke wani hali.

Karin Bayani: Yajin aikin gargadi a Tarayyar Najeriya

To sai dai kuma NLC na da jan aikin sauya tunanin 'yar uwarta TUC, wadda ta ce ba za ta taka rawa a cikin zanga-zangar ba. TUC dai ta ce babu shawara a bangaren NLC, a saboda haka ta zabi zama 'yar kallo cikin zanga-zanagr da ke zaman zakaran gwajin dafi kan farin jinin gwamnatin kasar da ke kokarin cika shekara guda da babban zabe. Dakta Muttaka Yusha'u dai na zaman shugaban wayar da kai da gangami a kungiyar NLC na kasa, kuma ya ce babu gudu babu ja da baya komai runtsi.

Najeriya | NLC | TUC | Zanaga-Zanga
'Yan kungiyar Kodogon Najeriya sun saba fantsama kan titiHoto: Nasir Salisu Zango

Wannan ne dai karo na farkon da ake hango alamun rabuwa cikin gidan na kodago a Najeriya, tun bayan rikicin tattalin arzikin da ke neman rikidewa zuwa siyasa mai muni. Abun kuma da ke iya shafar karfi da kila karsashin masu kodagon kasar da a baya kan tilasta gwamnatin ga tashi a tsaye. Kokarin zuwa ga bukata ko kuma neman mafitar matsi na tattalin arziki, kundin tsarin mulkin kasar dai ya tabbatar da 'yancin titi a tsakanin masu kodagon da ma ragowar jama'ar cikin gari.

Karin Bayani: Janye zanga-zangar neman sauyi a Najeriya

Shi kansa kokarin jan kunne na jami'an tsaro bisa yiwuwar tayar da hankali dai, a fadar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman shugaban Hukumar Gudanarwar Kungiyar Amnesty International mai kare hakki dan Adam a Najeriyar ya saba da muradun dimukuradiyyar kasar a halin yanzu. Masu mulki na kasar dai na a tsakanin kyale masu zuciyar mai tsummar kai wa ga tituna cikin bacin rai, ko kuma fuskantar rikicin da ka iya kai wa ga kara ciwo bisa ciwon da ke kasar a halin yanzu.