1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun janye yajin aiki

Binta Aliyu Zurmi
October 3, 2023

Manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC sun janye tsunduma yajin aiki na kasa baki daya da suka ce za su fara a yau na wucin gadin kwanaki 30.

https://p.dw.com/p/4X4Fm
Nigeria Protest NLC Abuja
Hoto: Uwais/DW

Matakin na NLC da TUC na zuwa ne bayan wata ganawa da suka yi da mahukunta Najeriya a jiya Litinin.

Dama tun kafin yanzu, gwamnatin Najeriya ta shirya karin albashi na wucin gadi ga ma'aikatan gwamnatin tarayya domin rage radadin matsin tattalin arziki wanda zai taimaka shawo kan kungiyoyin kwadago su janye kudirin wannan yajin aikin da suka ce muddin suka fara har sai baba ta gani, wanda karin albashi na daga cikin sharuddan da suka gindayawa gwamnati.

Kungiyoyin sun dauki matakin shiga yajin aikin ne sakamakon matsin tattalin arzikida al'ummar kasar ke fama da shi biyo bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi tun bayan darewa madafun iko a watan Mayun da ya gabata, wanda kungiyoyin suka yi watsi da wannan mataki.