1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zangar-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

March 1, 2024

Ana zanga-zangar tsadar rayuwa ta kwanaki biyu a Najeriya da kungiyar kodago ta kira saboda mawuyacin halin da jama'a suka shiga sakamakon tashin farashin kayayyaki masarufi.

https://p.dw.com/p/4cwW3
Najeriya | Zanga-zangar tsadar rayuwa
Zanga-zangar tsadar rayuwa a NajeriyaHoto: SAMUEL ALABI/AFP

Mutane da dama a Najeriya sun amsa kira na shiga zanga-zangar da kungiyar kodago ta kasar ta kira domin kan tsadar rayuwa. A jihohi da dama na 'yan kungiyar kwadago ta kasa ta kammala gudanar da zanga zangar da ta shirya a kan tsadar rayuwa da lallacewar tsaro cikin tsastsaurar matakai,domin dakile ayyukan bata-gari da sauran wadanda ke neman tayar da zaune tsaye.

Karin Bayani: Samame a kasuwannin 'yan canji na Najeriya

Najeriya | Zanga-zangar tsadar rayuwa
Zanga-zangar tsadar rayuwa a NajeriyaHoto: AP Photo/picture alliance

Zanga zangar dai an gudanar da ita cikin tsauraran matakai inda aka ga jami’an tsaro sun kewaye da masu tattaki da sauran da ke kade-kaden domin samar da tsaro.

Za a kwashe kwanaki biyu ana wannan zanga-zangar domin nuna fushi da tashin farashin kayayyaki da neman ganin an kara albashi ga ma'aikata a kasar mafi yawa jama'a tsakanin kasashen nahiyar Afirka.