Tasirin Joachim Gauck a siyasar Jamus | Siyasa | DW | 17.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tasirin Joachim Gauck a siyasar Jamus

Bayan karewar wa'adin mulki daya na Shugaban kasa, tsohon Pastor kuma mutumin da ake darajawa, Joachim Gauck ya sauka daga mukamin Shugabancin kasa da ake yi wa kallon kujera ce ta je-ka na-yika ne.

Österreichs Bundespräsident Van der Bellen bei Gauck (picture alliance/dpa/M. Kappeler)

Tsohon Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck

Joachim Gauck ya kasance Shugaba kuma abin alfahari ga Jamus da kuma Jamusawa. Sabanin magabatansa biyu Horst Köhler da Christian Wulff da suka gaza kammala wa'adin mulkinsu, a nashi bangaren ya kammala na shi ne cikin kima. Kamalarsa da iko suna da nasaba da irin kalaman da ke fita a bakin shi lokacin da yake jawabai. Jawabansa dai na kasancewa masu daukar hankali ne da karfafa gwiwa. Ya yi kokarin jaddadawa Jamusawa irin rawar da ya zama su taka a idon kasashen dunuya, irin kallon da ake musu, a hannu guda kuma da abin da duniya take fata daga bangarensu.

A matsayin shi na wanda ya taba zama malamin addinin Kirista wato Faston choci dai, jawabansa tamkar wa'azi ne dake daukar hankali. Kasancewarsa mai tausayi, mutane basa sanin lokacin da hankalinsu zasu koma kansa. Duk da cewar da yawa basa kaunar wannan halayya tasa, ofishinsa ya samu daukaka sosai. Hakan ne kuma ya karawa wannan mukami nasa martaba.

Gauck ya kasance mutum mai magana bil hakki daga zuciyarsa, mai fitar da tunaninsa a fili, wanda mutane ke kauna da hankoron sauraron jawabinsa. Saboda halayyarsa na tausayi ya kan jajirce a kan duk abin da ya sanya a gaba musamman wanda ya shafi rayuwar al'uma. Hakan ne ma ya sa ya kauracewa halartar wasannin motsa jiki na Olympics lokacin sanyi a Rasha, a wani mataki na nuna adawarsa da siyasar mamaya na Moscow.

Haka lamarin ya ke dangane da kisan kiyashi da aka yiwa Armeniyawa  a Turkiyya a lokacin yakin duniya na daya, wanda aka yiwa lakabi da kisan kare dangi, da ya jagoranci lalacewar alakar diplomasiyya da Turkiya.  Kazalika na baya bayannan dangane da karbar 'yan gudun hijira da kuma kama dan jaridar Jamus Deniz Yücel da akya a Turkiyan.

Shugaban na Tarayyar jamus mai barin gado Gauck, ya kasance dattijo mai magana daya, mai sanin ya kamata, wanda kuma ya taka rawar dimokuradiyya, duk da cewar ofinsa ba shi da wani girman matsayi. Ya kasance mai hazaka da karfin hali, wanda ya iya yin fito na na fito da masu kyamar baki a gabashin Jamus, ya ki juya baya duk da yadda lamarin ya kara tsamari.

Joachim ya zama Shugaban Jamus a daidai lokacin da ya dace. Mutum mai magana a lokacin da ya kamata ya furta magana. Duk da cewar mukaminsa ba wani mukami ne da ba kasafai ake jinshi ba, ya cimma nasarar yin tasiri da taka muhimmiyar rawa a fagen siyasar Jamus. Shi yasa ake masa kallon dan gwagwarmayan kasa.

Saboda girma da ta cimmasa ne, Gauck ya ki neman zarcewa kan mukaminsa a karo na biyu. Amma Jamusawa da yawa za su gwammace ya ci gaba da zama a kan wannan kujera ta Shugaban kasar Jamus. Ana iya cewar sanin muhimmancin wannan mukami nasa, shi ne ya sa ya mika aikin ga wanda zai yi shi da gaske.