1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Turkiyya na taro kan makamashi

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 26, 2018

Ministan tattalin arziki da makamashi na Jamus Peter Altmaier ya bude taron makamashi karo na biyu tsakanin Jamus da Turkiyya a birnin Ankara da ke zaman fadar gwamnatin Turkiyyan.

https://p.dw.com/p/37FoY
Türkei, Ankara: Minister Albayrak trifft sich mit Finanzminister Altmaier
Ministan kudi na Turkiyya Berat Albayrak da ministan tattalin arziki da makamashi na Jamus Peter AltmaierHoto: Reuters/Handout

A jawabinsa yayin bude taron, Altmaier ya yi karin haske dangane da kokarin bunkasa dangantakar sabunta makamashin da ke tsakanin kasashen biyu. Altmaier ya kara da cewa Turkiyya da Jamus za su zamo abin kwatance dangane da batun na sabunta makamashi, yana mai yabawa mahukuntan na Ankara bisa kudirinsu na kasancewa wata cibiya ta samar da makamashin iskar gas tsakanin Turai da Asiya. Baki dayan kasashen biyu dai na Jamus da Turkiyya na dogara ne da shigo da makamashin iskar gas din daga kasar Rasha.