TARON KOLIN MAJALISAR DUNKIN DUNIYA NA SHEKARA SHEKARA. | Siyasa | DW | 21.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TARON KOLIN MAJALISAR DUNKIN DUNIYA NA SHEKARA SHEKARA.

A yau ne zaa bude taron kolin MDD a birnin New York,wanda zai dauki makonni biyu yana gudana.

Zauren Majalisar dunkin duniya.

Zauren Majalisar dunkin duniya.

Gabannin taron koli ta MDD na shekara shekara da zaa bude yau a birnin New York,sama da shugabannin kasashe 50 da MDD sun bayyana damuwansu dangane da karuwan gibi tsakanin kasashe masu arzikin masanaantu da matalauta,sai dai akwai sabanin raayi dangane da yadda zaa yaki talauci,musamman akasashe masu tasowa.

Acigaba da kokarinsu na ganin cewa duniya ta yaki matsaloli na talauci da ake fuskanta,shugabannin kasashen duniya sun bukaci a tilasta aiwatar da haraji wa kowane irin harka daya shafi kudi,da harkoki da suka shafi cinikin manyan makamai ,banda samarda hanyoyin rancen kudi daga kasashe domin yakan yunwa.

Suhabannin kasashen Faransa da Brazilsun jagoranci kasashe 110,wajen neman amincewansu kann sabon kudurin yaki da yunwa da talauci,tare da kara kudi domin inganta cigaba,amma Amurka taki bada goyon bayanta.

Sama da shugabannin kasashe 50 sukayi muhawara gabannin wannan taro a jiya a MDD,wanda ya maida hankali kann muhimman cigaba da aka sa mu tsakanin kasashen duniya,da hanyoyi da zaa samarda kudade domin yaki da talauci.Shugaba Jacques Chirac na Faransa yayi kira da daukan alkawi na tabbatar da wannan manufa nasu,ayayinda takwaransa Luiz Lula da Silva na Brazil yace,matsaloli na yunwa sun kasance batu na siyasa,daya dace asa fifiko akai.

Dayake hira da manema labaru dangane da matsayin naki da Amurka ta hau kann kudurin,Shugaba Lula yace Amurka ta dauki muhimmin mataki na tura wakilinta zuwa taron.

Sakatariyar dake kula da harkokin noma ta amurka Ann Veneman a muhawaran na jiya,tace gwamnatin ta bata amince da shirin sanya harajin kasa da kasa ba,domin zasu sabawa tsari irin na Democradiyya,kuma zai kasance abu mawuyaci wajen aiwatarwa.

Shugaba George W Bush na Amurkan dai yaki halartan tarurrukan shugabanin biyu daya gudana a jiya litinin,sai dai jawabinsa a taron kolin na da zai bude ayau,zai jaddada damuwan kasashen duniya,musamman a dai dai lokacin da kasar Iraki da Rikicin Lardin Darfur a Sudan ke cigaba tauya hakkokin jamaa.

Wani bangaren rahotan mdd da aka gabatar a watan febrairu,na nuni dacewa an samu karuwan gibi tsakanin kasashe masu arzikin masanaantu da kasashe matalauta ,cikin shekaru 40 da suka gabata,asakamakon hakan ne ake ganin cewa alummar duniya baki daya bazasu iya ganin tasirin cigaba tsakanin kasashen duniya da ake ikirari ba.Ayanzu haka dai sama da mutane Billion guda ne ke rayuwa kann kudi kasa da dala guda a kowane yini,a shekarata 2000,inji wannan rahoto na mdd.

Shugaba Chirac wanda ya je New York musamman domin halartan wannan taro,yace shida shugaba Silva na Brazil zasu gabatar da sabbin hanyoyi da zaayi amfani dasu wajen rage radadin talauci,koda yake taron bai haifar da wani da mai idanu ba.

Taron na jiya na mai zama sharan fage ne wa taron kolin majalisar dazai gudana badi,inda zaayi nazari kann irin nasarori da aka cimma daga taron daya gudana a shekara ta 2000,wadanda suka hadarda rage kusan rabin wadanda ke rayuwa cikin kuncin talauci matsananci,da inganta makarantar yara kanana,da samarda ruwansha mai kyau nan da shekarata 2015.

Zainab A Mohammed.