Taron kolin kungiyar EU a birnin Brussels zai duba batun Turkiya | Labarai | DW | 14.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kolin kungiyar EU a birnin Brussels zai duba batun Turkiya

Ana sa ran cewa a gun taron kolin a Brussels, shugabannin kasashen KTT zasu albarkaci kudurin da ministocin harkokin wajen kungiyar suka zartas a farkon wannan mako, inda suka yanke shawarar dakatar da tattaunawar daukar Turkiya cikin kungiyar ta EU. An dauki wannan mataki ne saboda kin da Turkiya din ta yi na bude tashoshin ta na ruwa da filayen jiragen sama ga kasar Cyprus, wadda memba ce ta EU. da farko shugaban hukumar EU Jose Manuel Barroso ya nunar da cewa idan ba´a yi hattara ba, tattaunawar da ake yi da nufin daukar Turkiyar cikin EU ka iya daukar sama da shekaru 15.