Taron kasa da kasa na kungiyar malaman makaranta a Berlin | Siyasa | DW | 26.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron kasa da kasa na kungiyar malaman makaranta a Berlin

A yau alhamis aka kammala taron kungiyar malaman makaranta ta kasa da kasa a birnin Berlin

A jawabinsa na bude taron dai sai da shugaban kasar Jamus Horst Köhler yayi tsokaci da cewar ilimi shi ne mabudin samun wadata da jindadin rayuwa da kuma karbuwa tsakanin jama’a ba tare da la’akari da tushen mutum ba Ya-Allah Bajamushe ne ko dan kasar Ghana, Ko China ko kuma Brazil:

“Bai kamata samun nagartaccen ilimi ya zama wani lamari na alfarma ba saboda nagartaccen ilimi wani bangare ne na hakkin dan-Adam. To sai dai abin takaici shi ne har yau duniya ta gaza wajen tabbatar da wannan hakkin ga kowa da kowa.”

Shugaban kasa na Jamus Horst Köhler ya kara da yin nuni da cewar a yanzu haka akwai kimanin yara miliyan tamanin a sassan duniya daban-daban ba su da ikon samun karatu na faramare, a sakamakon haka a yanzu kimanin kashi daya bisa biyar na manyan ba su iya rubutu da karatu ba. A shekara ta 1973 ne dai aka kafa kungiyar ilimi ta kasa da kasa tare da mazauninta a birnin Brussels a matsayin wata kungiyar hada-ka tsakanin ‘yan kodago da malaman makaranta kuma tana da membobi sama da miliyan talatin da suka hada da malaman makaranta da sauran jami’an ilimi a kasashe 160. Kungiyar masana al’amuran tarbiyya da kimiyya ta Jamus da ta malaman makarantun koyar da sana’ar hannu da kuma gamayyar ilimi da tarbiyya sune ke wakiltar kasar a wannan kungiya ta kasa da kasa. A lokacin da yake bayani game da muhimmin abin da kungiyar ta sa gaba Ulrich Thöne dan kwamitinta na zartaswa cewa yayi:

“A dukkan sassa na duniya akwai bukatar nagartattun makarantu masu yawa da gwamnati zata dauki nauyinsu. Ilimi dai shi ne muhimmiyar kafa mai ma’ana wajen kyautata makomar jin dadin rayuwar dan-Adam, saboda shi ne zai bude masa kofofi na sana’a. Ilimi kazalika shi ne kakkarfan makamin yakar talauci da yunwa da cututtuka da kuma kandagarkin yake-yake da ta’addanci.”

Shi kuwa John Eastes daga Afurka ta Kudu yayi tsokaci ne da ire-iren matsalolin da malaman makaranta ke fama da su a dukkan sassa na duniya inda ya ce:

“Akwai matsalar rashin da’a, wadda ke dada karuwa ga matsalar tsaro dake dada tabarbarewa a makarantu. Domin tinkarar wannan matsala wajibi ne a fito da wasu tsare-tsare na musamman da zasu tafi kafada-da-kafada a al’amuran ilimi. Amma zai dauki lokaci mai kafin a cimma biyan bukata.”