Taron ƙoli na ƙasashen Latinamirka da ƙungiyar EU a birnin Vienna. | Siyasa | DW | 12.05.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ƙoli na ƙasashen Latinamirka da ƙungiyar EU a birnin Vienna.

Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, za ta iya zamowa abin kwaikwayo ga ƙasashen Latinamirka. Shugaban ƙasar Mexico, Vicente Fox ne ya bayyana haka, a wani taron maneman labarai da a birnin Vienna inda ake gudanad da taron ƙoli na na ƙasashen Latinamirka da na Ƙungiyar Haɗin Kan Turai.

Shugabannin ƙasashen Latinamirka da na ƙungiyar Haɗin Kan Turai a taron.

Shugabannin ƙasashen Latinamirka da na ƙungiyar Haɗin Kan Turai a taron.

A taron ƙolin ƙasashen Latinamirka da na ƙungiyar EU da aka buɗe a birnin Vienna, sai da wata mai fafutukar kare muhalli ta sami damar kutsawa bayan shingen jami’an tsaro, har ta bayyana gaban jerin shugabannin da suka halarci taron, a lokacin da suke ɗaukar hoto. Evangelina Carrozza, ’yar ƙasar Argentina ce, wadda ta ce tana son ta bayyana wa shugabannin adawarta ne, ga aikin gina wata ma’aikatar sarrafa takarda, da ake yi yanzu a ƙasar Uruguay. Kai tsaye ne dai jami’an tsaro suka yi awon gaba da ita.

A cikin jawabin da ya yi a wani taron maneman labarai a birnin na Vienna, shugaban gwamnatin ƙasar Austriya, kuma mai karɓar baƙwancin taron, Wolfgang Schüssel, ya bayyana cewa „akwai dai bambanci tsakanin Latinamirka da Turai“. Masharhanta na ganin cewa, yana matashiya ne da bambancin ra’ayoyin da ake samu tsakanin ƙasashen nahiyar kudancin Amirkan. Amma a lokaci ɗaya kuma, shugaba Schüssel ya bayyana cewa, yankunan biyu na da wasu al’adu da manufofi na bai ɗaya da suka haɗa su. Ita dai Ƙungiyar EU, ba za ta yi shisshigi a harkokin ƙasashen Latinamirkan ba, inji shugaban na Austriya. Kazalika kuma ba ta damu ba, da yunƙurin da ƙasashe kamarsu Sin ke yi, wajen samun tushe a yankin. Kamar dai yadda shugaban ya bayyanar:-

„Ni dai ba mai goyon bayan hasashen da ake yi ba ne, wanda a lokuta da dama ake ta bugawa, inda ake ta yaɗa fargabar cewa, za mu rasa angizonmu a Latinamirka. Kuma za mu yi asarar kadarorinmu. A nawa ganin dai, mu ba masu reno ko kuma masu ba da umarni ga wasu ba ne. A daura da haka, mu abokan hulɗa ne da al’umman Latinamirka.“

Da yake mai da martani a madadin ƙasashen kudancin Amirkan, shugaban ƙasar Mexico, Vicente Fox, ya ce Latinamirka za ta iya yin kwaikwayo da haɗin kan Turai, musamman a wannan lokacin da tserereniyar samun fa’ida a huskar tattalin arziki da son zuci ke ta barazanar rarraba kawunan ƙasashen yankin na Latinamirka. Wannan bambancin da ake samu ma, shi ne dalilin da ke janyo jinkiri wajen ƙulla yarjejeniyar kafa kasuwa maras shinge tsakanin nahiyar Turai da Latinamirka, inji shugaban na ƙasar Mexico. A birnin Vienna ma, ana iya gani a zahiri, irin bambance-bambancen ra’ayoyin da ke tsakanin ƙasashen Latinamirkan, wato tsakanin masu ba da fiffiko ga kariya a fannin tattalin arziki kamarsu shugaba Evo Morales na Boliviya a ɓangare ɗaya, da kuma masu bin aƙidar kasuwar jari-hujja kamarsu shugaba Fox na Mexico a ɗaya ɓangaren. A ganin shugaban na Mexico dai, gindaya shinge da yaɗa aƙidar guguzu a harkokin tattalin arzikin yankin, ba za su janyo wa kowa fa’ida ba. Kamar yadda ya bayyanar:-

„Yin hakan, na iya kasancewa wani babban cikas ga bunkasar tattalin arziki da ci gaban ƙasashenmu. Kuma ba matakin da ya dace ba ne wajen yaƙan talauci. Wani salo ne kawai na kambama kai.“

Ƙasar Boliviya kuwa, tana nan tana ci gaba da matakan kariyar da take ɗauka. Bayan mai da duk masana’antun haƙon hayaƙin gas ƙarƙashin ikon gwamnati, shugaba Morales ya kuma ce zai faɗaɗa wannan matakin zuwa wasu sassan tattalin arziki na ƙasar gaba ɗaya. Kazalika kuma, shugaba Hugo Chavez na Venezuela, shi ma mai matuƙar adawa ne ga aƙidar jari-hujja, musamman kuma ga manufofin Amirka a yankin. Yana samun farin jini dai a taron maneman labarai da kuma tarukan da ƙungiyoyin sa kai ke gudanarwa.

A cikin nasa jawabi ga taron, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya yi gargaɗin cewa, a hulɗoɗin tattalin arziki na ƙasa da ƙasa, korar masu zuba jari da ɗaukan matakan ɗora hannun gwamnati kan masana’antu ba zai janyo wata fa’ida ga ƙasashen da ke yin haka ba. Abin da ke da muhimmanci shi ne, a yi tanadin hulɗoɗin tattalin arziki da albarkatun ƙasa ta yadda ƙasashen da lamarin ya shafa da al’ummansu za su ci moriya. Ana bukatar yarda a hulɗoɗin kasuwancin ƙasa da ƙasa. Sabili da haka masu zuba jari ma na bukatar tabbacin ganin cewa, yunƙurinsu zai janyo musu fa’ida a lokaci mai tsawo, inji Kofi Annan. Ya kuma ƙara da cewa, kamata ya yi, nahiyar Turai da ƙasashen Latinamirka su fi mai da hankali a tsarin manufofin tattalin arzikinsu, wajen samar wa matasa aikin yi da kuma samar musu wata hanya daban, wadda za ta zamo musu zaɓi ga shan ganye da miyagun ƙwayoyi da kuma hana su aikata miyagun laifuffuka.

 • Kwanan wata 12.05.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu08
 • Kwanan wata 12.05.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu08