Takaddama tsakanin Turkiya da Jamus | Labarai | DW | 01.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama tsakanin Turkiya da Jamus

Gabanin majalisar dokokin Jamus ta amince da kudiri kan batun kisan kiyashi na Armeniyawa, Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya gargadi Jamus din da kada ta kuskura ta zartas da kudirin.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Wannan kudiri dai in har majalisar dokokin ta Jamus ta amince da shi, zai nunar da cewa Turkiyan ta aikata kisan kiyashi a kan Armeniyawa, a yayin yakin duniya na farko da aka yi a shekara ta 1915. Erdogan dai ya yi gargadin ne yayin wata tattaunawa da suka yi da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta wayar tarho, inda ya ce in har majalisar dokokin Jamus din ta yi gigin amincewa da wannan kudiri, to tabbas a shirye Turkiya take ta yanke duk wata hulda ta siyasa da tattalin arziki da ma ta soji tsakaninta da Jamus din. Turkiya dai ta dage kan cewa babu wani batun kisan kiyashi, kana yawan mutanen da suka rasa rayukansu a wannan lokaci bai wuce 500,000. Sai dai a hannu guda Jamus na cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a yayin yakin duniya na dayan, sun kai miliyan guda da rabi. Wannan batu dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Jamus ke bukatar taimakon Turkiya kan batun kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai da mafi yawa daga cikin su ke son shiga Jamus.