1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Za a yaki matsalar kyamar Yahudawa

Ramatu Garba Baba
July 1, 2021

Jamus da Isra'ila sun kara jadadda matakinsu na yakar matsalar kyamar Yahudawa a yayin ziyarar da Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya kai kasar.

https://p.dw.com/p/3vt6r
Israel | Besuch Bundespräsident Steinmeier
Hoto: Ronen Zvulun/REUTERS

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da ke ziyarar aiki a Isra'ila, ya sami kyakyawar tarba daga takwaran aikinsa Reuven Rivlin bayan da ya isa kasar, a jawabinsa, Shugaba Rivlin ya yabawa Jamus kan tsayawar da ta yi kai da fata don yakar matsalar kyamar Yahudawa da al'ummar kasar ke fuskanta a cikin kasar. Ya kuma ce, dangantakar da suka kulla ya samo asali tun daga lokacin da suka yaki bala'in yakin duniya na biyu, da ya so ya shafe Yahudawa daga doron kasa.

Kasashen biyu sun fuskanci manyan kalubale bayan yakin duniyan, sai dai sannu a hankali al'amura suka soma daidaita bayan da Jamus ta yi ta neman afuwa tare da biyan diyya a sakamakon asarar rayuka da dukiya da Isra'ila ta tafka. A kowacce ranar 27 ga watan Janairu na kowacce shekara, Jamus ke gudanar da bikin tunawa da kisan kare dangi da gwamnatin 'yan Nazi a Jamus ta yi wa Yahudawa kimanin miliyan shida.