Steinmeier: EU ka iya rushewa idan Birtaniya ta fice | Labarai | DW | 15.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Steinmeier: EU ka iya rushewa idan Birtaniya ta fice

Ministan harkokin wajen Jamus ya ce ficewar Birtaniya daga EU ka iya zama mafarin rugujewar kungiyar ta Tarayyar Turai.

Deutschland Berlin Frank-Walter Steinmeier und Jean-Marc Ayrault

Steinmeier (dama) da Ayrault (hagu) a taron manema labarai a Berlin

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce kuri'ar raba gardama da al'ummar Birtaniya za su kada a mako mai zuwa game da yiwuwar ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai EU ka iya zama mafarin rugujewar kungiyar ta Tarayyar Turai. Steinmeier ya fada wa wani taron manema labarai na hadin guiwa da takwaransa na Faransa Jean-Marc Ayrault, a wannan Laraba cewa matukar Birtaniyar ta fice, to hakan zai girgiza EU ta yadda za ta bukaci tabbaci tsakanin 'ya'yanta cewa za su cigaba da zama tare, kana nasararorin da ta samu bayan tsawon shekaru gommai na hadaka, ba za su kai ga wargajewar kungiyar ba a karshe. Ministocin biyu sun yi fatan cewa 'yan Birtaniya za su amince da cigaba da zama cikin EU a kuri'ar raba gardamar da za su kada a ranar 23 ga watan nan na Yuni.