Sigmar Gabriel ya yi kira da samar da runduna mai karfi a gabashin Ukraine | Labarai | DW | 04.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sigmar Gabriel ya yi kira da samar da runduna mai karfi a gabashin Ukraine

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya yi kira da mika ikon gabashin Ukraine ga sojojin kiyaye zaman lafiya.

Ukraine Kiew Außenministertreffen Sigmar Gabriel und Pawlo Klimkin (picture-alliance/photothek.net/I. Kjer)

Sigmar Gabriel da Pavlo Klimkin a birnin Kiev

Ministan harkokin wajen tarayyar Jamus Sigmar Gabriel ya ce kamata ya yi sojojin kiyaye zaman lafiya su karbi ragamar iko da ilahirin yankin Donbass da ke gabashin kasar Ukraine. Gabriel ya nunar da haka ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi da takwaran aikinsa na Ukraine Pavlo Klimkin a birnin Kiev.

Gabriel ya ba da tabbacin cewa Jamus da sauran kasashen da ke a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya za su yi aiki tare don ganin an girke wata tawagar kiyaye zaman lafiya a Donbass.

"Ya kamata a samu wata tawagar soji mai karfi ta duniya da za ta kasance a ilahirin yankin da aka mamaye, ba wai kawai su kasance masu gadin wani karamin yanki kawai ba, in an yi haka tamkar an kirkiro wata sabuwar iyaka ke nan a Ukraine."

Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen Ukraine Pavlo Klimkin ya ce har yanzu ana cikin zaman zullumi a yankin. Ya ce duk da shirin tsagaita wuta amma har yanzu ana samun harbe-harbe da ke sanadin rayukan mutane musamman sojoji.