Shugabar gwamnati Merkel ta Jamus ta fara ziyara a Brazil | Labarai | DW | 20.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabar gwamnati Merkel ta Jamus ta fara ziyara a Brazil

Batun yaki da sauyin yanayi da satar bayanai ta kafat intanet na cikin abubuwan da zasu dauki hankali a wannan ziyara.

Deutschland IFA in Berlin Angela Markel

Shugaba Angela Markel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta isa Brazil a ziyarar da ta fara ta kwanaki biyu tare da wasu mambobin majalisar zartarwarta inda zasu tattauna da shugaba Dilma Rousseff kan batutuwa da suka shafi sauyin yanayi da batutuwa da suka hadar da tsaron bayanai a shafukan intanet.

Irin wannan tattaunawa dai na zama irin ta farko da bangarorin gwamnatin daga kasashen Turai da Amirka ta Kudu da tattalin arzikinsu ya banbanta da saura a yankunansu zasu zauna kan wannan batu.