Shugaba Goodluck ya bukaci hakurin ′yan Najeriya ranar zabe | Labarai | DW | 28.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Goodluck ya bukaci hakurin 'yan Najeriya ranar zabe

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, ya bukaci hakurin al'umar kasar kan duk wasu kura-kuran da za a iya samu a zaben da ke gudana a halin yanzu a fadin kasar.

Shugaban na Najeriya wanda kuwa shi ne dan takaran jamiyyar PDP a zaben, ya yi kiran ne yayin da ya fuskanci tangardar tantancewa daga na'urar tantance masu zabe da safiyar yau, a mazabarsa da ke garin Otuoken kundancin jihar Bayelsa.

Shugaba Jonathan dai ya ce bai damu ba, duk da tangardar da aka samu ganin cewa karon farko ne da ake amfani da wannan fasaha a kasar.

Jam'iyyar PDP mai mulkin kasar dai tun farko ta nuna tababa kan ingancin na'urorin tantance masu zaben, ko kuma kwarewar wadanda za su yi amfani da su a lokutan na zabe.