Shugaba Assad na Siriya ya fara sabon wa′adi na mulki | Siyasa | DW | 16.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugaba Assad na Siriya ya fara sabon wa'adi na mulki

Kasashen Yammacin Duniya sun fara dawowa daga rakiyar tsagerun Siriya saboda yadda masu kaisfin kishin addini suka fara yi wa kasashen barazana

Ci gaba da fadada yakin da kunkiyoyin tsageru masu ikirarin yin jihadi ke yi, da sunan kafa daular Islama a Siriya da Iraki ya sauya daukacin yadda duniya ke kallon rikicin kasar Siriya baki daya. Domin Tun fara yakin basasan kasashen Yamma na daukar Shugaba Bashar al-Assad a matsayin makiyinsu, amma yanzu sun gwammaci yin hulda da shugaban maimakon tsageru marasa alkibla.

Dama tun watannin da suka gabata tsohon shugaban rundunar leken asirin Amirka ta CIA ya ce da irin abin da suke ganin na faruwa, sun nasarar Assad a yakin Siriya ita ce mafi alheri ga kasashen Yamma. Albert Stahel wani masani ne da ya kware kan rikicin Siriya:

"A Siriya ina ganin lamarin tamkar ya sauya, Mutum zai iya cewa, kasashen Yamma na kare Assad ne a yanzu, ko kuma ace dai an samar da zaman lafiya. Ta yadda Assad zai iya iko da musamman birnin Damaskus, da Aleppo, kana a kare kasar Jordan."

An dade ana ba da rahotannin cewa shugabannin jami'an leken asirin kasashen Yamma na tattauanawa da gwamnatin Shugaba Assad. Tuni wata kafar yada labaran Jamus ta ba da rahoton tun a bara jami'an leken asirin Jamus suka fara yin magana da gwamnatin Assad, haka wani jami'in leken asirin Siriya ya kai ziyara kasar Norway inda ya gana da jami'an gwamnati cikin sirri.

Sai dai akwai wadanda ke cewa ya kamata kasashen Yamma su yi hattara da yin zabi tsakanin Shugaban Bashar al-Assad wanda ya fara sabon wa'adi na uku na mulki na karin wasu shekaru bajkwai da mayaka mafi yawa masu kaisfin kishin addin Islama.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin